Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Shaikh Isma'il Yusha'u Kudan.
Rana ta 5
A yau Talata 6 ga watan Ramadhan dai-dai da 28/3/2023 an shiga rana ta Biyar a karatun littafin "Zadul Qulub Fiy Shahrillah" wanda Shaikh Isma'il ke gabatarwa duk shekara a watan Ramadan a Husainiyyatu Rasulil-Akram(S) dake unguwar Furoja a garin Kudan. Karatune wanda ke koyar da al'umma yadda zasu gabatar ingantacciyar ibadar watan Ramadhan (azumi) da ladubbansa.
MAUDHU'I: A yau Shaikh yayi karatu ne dangane da muhimmancin sada zumunci ta hanyar ziyara musamman a watan Ramadan, da yadda Allah da Manzo su muhimmantar da al'amarin ziyara ga Muminai. Malam ya kawo ruwayoyi daga gidan Annabta da suke magana dangane da muhimmancin ziyara a addini, ta yadda Allah ke tsawaita rayuwar ma'abocin ziyara. Malam Yace wannan ma wata hanya ce ta bawa zai kara kusanta kansa ga Allah da sauran Muminai a watan azumi.
ABIN LURA: Ana gabatar da karatun ne daga karfe 5:00 na yamma zuwa 6:00 na yamma, sannan karatun ya kasu kashi 2 ne, bangaren karatun littafin "Zadul Qulub Fiy Shahrillah" da kuma "Hukunce-Hukuncen Azumi", sannan daga karshe a raba hadiyyar abin bude baki (dabino).
— R.A.C.F
28/3/2023