@_Ma'asuma Nigerian Update
Part (1)
Tare da Abokin Aikin Mu
EngMuhammad Hamza Usman Yarsakakea ✍️
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Tun kamar 'yan Juma'o'i biyu ko uku da suka wuce, na so na dan
yi magana a kan halin da tattalin arziqi da matsi, wanda
mutanen qasar nan suka shiga ciki. Don ko ba komai shi ne
yanzu ya zama babbar matsalar da ta shafi kowa da kowa. Ko a
zauren hira ne, ko a gidan rediyo ne ko jarida, ko kan titi ko
cikin mota ne, matasalar rayuwa ta riga ta sha wa kowa kai,
kuma ta xauke musu hankulansu gaba xaya, babu wani abin
tattaunawarsu sai shi (tattalin arziqin).
Kuma baya ga bayanai da rediyo da jaridu ke yi, har ma
qungiyoyi da dama sukan qira tarurruka su yi waxansu bayanai
kan waxannan matsalolin. Alal misali, akwai waxanda suka kira
taro don jin ra'ayoyin Malamai dangane da ko ya halatta a yi
cinikin kuxi da kuxi? Don suna tsammanin yana daga cikin
dalilan da ya sa mutane suka faxa cikin wahala. Suna ganin babban dalili shi ne don an sauya takardun kuxin Nijeriya a
cikin kuxaxen duniya, wanda ya janyo faxuwar kuxin, wanda
yanzu ba su iya sayen wani abu (mai kima) daga waje. Kuma bayan wannan har ta kai ma mutane sun fara nuna
damuwarsu ta kowace hanya. Kamar yadda muke ji a wasu
wurare ma har ta kai sun yi yamutsi, kuma har da kashe-kashe
da qone-qone.
ADDININ MUSULUNCI YA SHAFI DUK RAYUWA NE:
To, da farko dai magana kan al'amarin halin rayuwa, maudu'i ne
na Musulunci; kuma Masallaci wuri ne wanda ya cancanci a yi
magana a kai, ba siyasa bace, ba kuma son rayuwar duniya bane, tunda yake Allah Ta’ala shi ne ya halicce mu, ya kuma
sanya mu a wannan qasa. Kuma ya halitta mana duk abin da
muke buqata har iyaka rayuwarmu. Kuma ya sanya cewa a
rayuwar tamu akwai wasu qa'idoji da sharuxxa waxanda za mu
bi, kuma in mun bi waxannan qa'idoji da sharuxxa, to mun bi
addinin (musulunci) kenan, mun kuma bauta masa.
Qa'idoji da dokokin sun haxa da halin rayuwarmu a
kullum, kamar wurin kwananmu, da suturarmu, da abincinmu;
duk akwai dokokin Allah a ciki. Kai hatta ma hulxa a
tsakaninmu yamu-yamu, kamar ciniki da sana'o'i, duk akwai
qa'idojin addini a ciki.
Saboda haka addinin Musulunci akwai nasa fagen, wanda
yake Alqur'ani ya qaryata cewa addini ya shafi dangantakar
mutum da Ubangijinsa ne kawai ta fuskacin addu'o'i da
sadakoki. Don in muka duba ayoyi da hadisan Manzon Allah
(S) suna magana kan abin da ya shafi rayuwa gaba xaya ne.
Saboda haka magana akan wannan, wani abu ne da ya shafi
addinin Musulunci gaba xaya. Muna iya ganin cewa a cikin
shika-shikan Musulunci akwai Sallah da Zakka. Kuma sau da
yawa Allah yana gwama Sallah da Zakka a wurare dabandaban. “Ku tsai da Sallah, ku ba da Zakka”.
Sallah alamin ibada ne wadda take tsani tsakanin bawa da Ubangijinsa. Wanda yake ita Sallah ita ce babba daga cikin wadannan ibadodi. Zakka kuma tana alamin adala (adalci) da ke
tsakanin mutane waxanda ke zaune a wuri guda, tunda akan
karbi wani abu da ke tsakanin masu shi zuwa ga hannun marassa shi, domin kar ya zama wasu sun tafi da ‘Hazzozi’ Kuma ya zo a cikin Alqur'ani, Allah (T) yana cewa; “Da
Allah zai buxe qofar arziqi a duniya, da mutane sun yi shisshigi
a bayan qasa, amma yana sauqarwa daidai gwargwado ne ta
yadda ya ga dama”. Wato shisshigi a nan shi ne, da Allah Ta’ala
ya azurta kowa, to da wasu kila bayan gidansu da burodi za su
share saboda wadata (maimakon takarda), sai a nemi burodi
kawai a share da shi saboda shisshigi, ko kuma inda zai zauna
sai ya yi na zinariya.
Amma muna iya ganin azzalumai waxanda suka yi
shisshigi, inda ma za su yi bayan gida sai a yi masu na zinariya,
ko kuma inda za su xora qafafunsu a kan kujera, sai a yi na
zinare. Da a ce Allah zai yalwata arziqi, wato Zinari da Azurfa
su wadata, da xan Adam ya yi shisshigi, da bai ga darajar abin
da aka ba shi ba. To amma Shi Allah yana sauqar da shi daidai
gwargwado. Bai yi yawan gaske da zai kai su ga xagawa ba, bai
kuma qaranta qwarai yadda zai kai su ga shiga wani
matsanancin hali ba.
Idan har ya zamana cikin abin da Allah yake saukarwa xin
nan, domin mutane su samu abin da za su tsaya da rayuwarsu ta
yau da kullum ya zama ya gagara, sun rasa, to wasu ne suka
qwace masu nasu hakkin, tunda Allah Ta’ala yana saukar da
daidai gwargwado. In ka ga wasu ba su da shi, to wasu masu shi
ne suka qwace haqqin wasu, tunda an saukar da shi ne daidai
gwargwadon buqatun (kowa).
To kuma za mu ga cewa Allah Ta’ala sau da yawa ya
yalwata arziqi da cewa wani abu ne daga gare Shi. Da ma Allah
Shi ke saukar da ruwa daga gare shi, Shi ke kuma tsirar da tsirrai. Abincinmu yana daga tsiro ne da ke tsirowa daga qasa,
da kuma dabbobi da muke hawa, su sha ruwa, su ci abinci.
Kazalika ma ya bizne a qasa; shi ya bizne qarfe da Zinare
zamu cigaba in sha Allah kukasance da bibiyarmu a shafin mu na Ma'asum Nigerian News Update
Real Naseer Umar Alhassan
Na Shaheeda Bawan Allah
22/8/1444. 14/3/2023