Idan Kaki Auren Su Wa kake So Ya Aure Su..??

 


FA'IDODIN AUREN 'YAR'UWA (sister) !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


IDAN KA QI AURENSU WA KAKE SO YA AURE SU


Ma'anar kalmar 'yar'uwa (sister) a gwagwarmayance yana dauke ne da ma'anoni biyu wanda kowanne daga cikinsu na da nasa ma'anar. Akwai ma'ana ta Lugga da kuma ta sharia.


'YAR'UWA A LUGGA:- Idan kaji ance' yar'uwa, a Lugga ana nufin dukkan matar dake da wilaya ga wani jagora mai tamassuki ga waliccin Limaman sharia goma sha biyu (A'imma). Wannan jagora kuma ko da daga cikin wacce Qasa ce yake jagoranci.


'YAR'UWA A SHARIA:- A sharia in kaji ance 'yar'uwa ana nufin mace wacce ke da wilaya ga jagora mai tamassuki ga Limaman shiriya goma sha biyu (12), kuma tana tarayya cikin dukkan ayyuka wandanda ake aiwatarwa/gudanarwa cikin harkar muslimci. Misali:-


- Zuwa makaranta.


- Halartar tarurruka.


- Zuwa wajen Ta'alimat.


- Bayar da imfaqi.


- Halartar guraren addu'o'i , D.S


To, rubutunmu na yau mun gina shi ne kan wannan aji na biyu mai dauke da wadannan siffofi da muka bada misali da su.


FA'IDODIN AUREN 'YAR'UWA


Fa'idodin dake qunshe cikin auren 'yar'uwa abu ne wanda ba zai qirgu ko lissafu ba, sai dai mu kawo misalai kawai daga cikinsu kamar haka:-


(1)- QARFAFA GINI:- Sanin kowa ne cewa kafin bayyanar sharafuddeen Sayyid Zakzaky (H) ba a san wata mace wai ita 'yar'uwa ba, har sai bayan bayyanarsa ce yayi wannan gini kuma almajiransa suka taimaka masa wajen qyayata shi. Saboda haka a duk lokacin da ka auri 'yar'uwa haqiqa ka taimaki harka ne tare da qarfafa wannan gini da aka gina.


(2)- TAIMAKON KAI-DA-KAI NE:- Duk wanda ya auri 'yar'uwa haqiqa ya taimaki wanda ke da haqqi ne wajen daukar nawinta da bata tarbiyya. Haka kuma shi ma zai sami wanda zai taimaka masa wajen cigabantar da tarbiyyar tasa ('ya) wacce ya shafe shekaru yana tarbiyyantar da ita kan wannan aqida tasa tun daga halin quruciya har zuwa lokacin da zai rabu da ita.


(3)- SAMUN SAUQI WAJEN TARBIYYANTARWA:- A duk lokacin da ka auri 'yar'uwa haqiqa za ka sami sauqi wajen tarbiyyantar da ita, domin tun kafin zuwanta hannunka tana da mafi girman tarbiyyar da kake so ka bata. Abinda za kayi kawai shine dorawa daga inda aka tsaya. Sannan kuma za ta zama mai bada tarbiyya ga 'ya'yan da Allah ya baku bisa koyarwar Ahlul-Bait (A.S).


(4)- QARFAFA JUNA:- A daidai lokacin da kake qarfafarta wajen aikata ayyukan gwagwarmaya haka kuma ita ma za ta zama mai qarfafarka yayin da taga gazawarka ta wani bangare.


(5)- SABAWARKU BA TA HANA AYYUKAN GWAGWARMAYA:- Abu ne mawuyaci ace dadin zama zai hana samun sabani wani lokaci kamai qanqantarsa. Saboda haka ko da kun sami sabani ba zai hana ta zuwa makaranta ko ta'alim ko zuwa addu'a ba, domin tuntuni ta san ayyuka ne wajiban dake kanmu wadanda ba a neman iznin wani wajen aiwatar dasu. D.S


ILLOLIN RASHIN AURENSU


Abu ne wanda ake yawan jin sa ko ganinsa ana yawo da shu cikin yanar Gizo cewa 'yan'uwa (sisters) na da girman kai, suna da buri a rayuwarsu kuma basu iya soyayya ba.


Idan batun girman kai ne ko buri da ake magana kansa sai nace, in dai hakane ai kuwa cikin 'yan'uwa (brothers) ma ana samun irin wadannan, domin ba duk aka hadu aka zama daya ba. Batun rashin iya soyayya kuwa ban sani ba ko yarda a zauna guri daya ana hada jiki ne ba sa yi ko kuma ba sa yarda ne a riqa rungumarsu kamar yadda wasu ke yi ? Idan kuwa hakane sai nace, ai dama haka koyarwar harka take, wato bata yarda da irin abinda samari ke so a riqa yi musu ba. Amma duk mace mai sonka ta san abubuwa da za ta nuna maka masu alamta soyayya, ta hanyar furuci ne ko ta hanyar rubutu.


Saboda haka daga cikin illolin sun hada da:-


(1)- RUSHE GINI:- An dora  su akan tarbiyya mai kyau kuma aka gina su kan tsabtatacciyar aqida sannan aka bar su suka fada hannun wanda zai rushe su. Ya zama munyi gini kuma muka rusa shi da kanmu ba tare da mun gina wanda ya fi shi ba.


(2)- YAQAR KAI-DA-KAI NE :- Abu ne sananne ana sukarmu kan wata aqida wacce ba ma aikatata, sannan ana qyamatarmu da 'ya'yan namu mata. To, idan aka ce munyi watsi dasu ta hanyar rashin auren su yayin da wasu ke qyamatarsu, me ake so kenan a gani cikin rayuwarsu ? Wannan ya zama yaqar kai-da-kai kenan.


(3)- ABINDA KAYI SHI ZA AYI MA:- Idan kace kai ba za ka auri 'yar'uwa ba alhali suna nan zube a qasa suna buqatar samun 'yan'uwa (brothers), to, da sannu za a wayi gari kaga 'ya'yanka ko  'yan'uwanka (mata) zube a gabanka ba tare da sun sami dan'uwan da zai nuna tana sonsu ba.


Muna ganin haka ko muna ji, 'yar'uwa ta gama karatunta na sakandari 18 ko 20yrs, ta qara shekaru biyar a gida ba tare da dora wani karatun ba kuma ba tare da tayi aure ba. Kowa yaga haka dai ya san ba wai son rai bane.


Kafin ajiye alqalamina zan juyo kanku 'yan'uwa mata (sisters), da gaske abinda ake fada a kanku na batun girman kai ko buri ana samunsa cikinku kamar yadda ake samu cikin 'yan'uwa (brothers).


Akwai daga cikinku wadanda Idan sun ga sunyi karatu sai suce ba za su auri wanda bai kai su a matakin karatu ba. Daga nan sai buri ya shigo cikin zuciyarsu na cewa babban ma'aikacin hukuma suke so, ko kuma wani hamshaqin mai kudi wanda zai riqa daukar su a mota zuwa wajen programmes, sun manta da cewa babansu Achaba yake hawa ko ya nemi agaji (lift), ita kuma mamarsu ta hanyar a daidaita sahu take zuwa program ba tare da hakan ya dame ta ba. Wannan dabi'a ce ta Amawa, amma ta ratsa cikin 'yan'uwa mata masu da'awar kawo gyara.


Wasu kuma cewa suke, ba za su auri wanda ke da mata ba, masu sassaucin cikinsu kuma suce sai dai su a tarar da su amma ba dai su su tarar ba. Abinda suke mantawa shine, wataqila mamarsu ba ita kadai ce tare da mahaifinsu ba. Sannan kuma tunaninsu ya kasa kaiwa kan ko na mutuwar aure akwai mutuwa ta al'ada, musamman ma cikin 'yan gwagwarmaya.


A tunaninki 'yar'uwa kina gani bayan kin haifi 'ya'ya Bihar sai aurenki ya qare ko mai gidanki ya rasu, kina ga saurayi marar aure zai zo wajenki da sunan yana sonki da aure ? Ko kuma duk mai sonki sai ya sake (divorce) matarsa kafin ya aure ki ?


AYI NAZARI DAI 'YAN'UWA MATA


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da ✍🏽 Ado Isah Guda.


     (08137925034)


24th March, 2022/  21st Sha'aban, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post