Ganin Falalar Imam Aliy (a.s) Ta Jawo Rabuwar Kan Musulmi !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


BASU RABU BA HAR SAI BAYAN SANIN WANNAN FIFIKO YA ZO MUSU


Allah (T) ke daukaka darajar bayinSa ta dukkan fuskar da Yaso, yakan fifita wani a ilimi, wani a dukiya, wani sarauta, wani a nasaba, wani kuma daraja ce irin ta Annabta ko Imamanci.


Babu wata falala da Allah zai bawa mutum ba tare da an sami masu yi masa hassada ba, mafi girman wacce aka fi hassada a kanta ita matsayi na tsarkaka da kuma samun daukaka wajen Allah. 


Kafin wafatin Annabi (S. A. W. W) ba a sami rabuwar kai ta zahiri tsakanin musulmi ba sai dai wacce ake yinta a boye bayan jin falalolin Imam Ali (A. S) dake fitowa daga bakin fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W).   Babbar rabuwar kuma ita ce wacce ta auku bayan fakuwar wanda ake yiwa wahayi (S. A. W. W) yadda aka canza daga abinda yayi musu umarni a kansa. . 


Ya zo cikin riwaya game da fadin Allah (T) : " KUMA BA SU RABU BA..........."


علي بن ابراهيم القمي (رحمه الله)- قَوْلُهُ تَعَالَى وَ ما تَفَرَّقُوا إِلَّا مِنْ بَعْدِ ما جاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْياً بَيْنَهُمْ قَالَ لَمْ يَتَفَرَّقُوا بِجَهْلٍ وَ لَكِنَّهُمْ تَفَرَّقُوا لَمَّا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ وَ عَرَفُوهُ فَحَسَدَ بَعْضُهُمْ بَعْضاً وَ بَغَي بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ لَمَّا رَأَوْا مِنْ تَفَاضُلِ أَمِيرِالْمُؤْمِنِينَ (عليه السلام) بِأَمْرِ اللَّهِ فَتَفَرَّقُوا فِي الْمَذَاهِبِ وَ أَخَذُوا بِالْآرَاءِ وَ الْأَهْوَاءِ ثُمَّ قَالَ عزَّوَجَلَّ وَ لَوْ لا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِنْ رَبِّكَ إِلي أَجَلٍ مُسَمًّي لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ قَالَ لَوْ لَا أَنَّ اللَّهَ قَدْ قَدَّرَ ذَلِكَ أَنْ يَكُونَ فِي التَّقْدِيرِ الْأَوَّلِ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ إِذَا اخْتَلَفُوا وَ أَهْلَكَهُمْ وَ لَمْ يُنْظِرْهُمْ وَ لَكِنْ أَخَّرَهُمْ إِلَى أَجَلٍ مُسَمًّي الْمَقْدُورِ وَ إِنَّ الَّذِينَ أُورِثُوا الْكِتابَ مِنْ بَعْدِهِمْ لَفِي شَكٍّ مِنْهُ مُرِيبٍ كِنَايَةٌ عَنِ الَّذِينَ نَقَضُوا أَمْرَ رسول الله (صلى الله عليه و آله).


Daga Aliyu Bn Ibrahim Al -Qummiy (R. A), fadinSa (T) :


" KUMA BASU RABU BA HAR SAI BAYAN ILIMI YA ZO MUSU BISA ZALUNCI TAAKANINSU. " Yace :


" Ai basu rabu bisa jahilci (rashin sani) ba, sai dai su sun rarrabu ne yayin da Ilimi yazo musu kuma suka san shi, sai sashensu suka riqa yiwa sashe hassada, kuma sashe suka riqa qetare iyaka kan sashe yayin da su kaga falalar shugaban muminai (A. S) bisa al'amarin Allah (ganin damarSa). Sai suka rarrabu cikin Mazhabobi da kuma su kayi riqo da ra'ayoyinsu da bin son ransu. Sa'an nan mai girma da daukaka yace :


" DA BA DON WATA KALMA DA TA GABATA DAGA UBANGIJINKA BA ZUWA WANI LOKACI AMBATACCE DA MUNYI HUKUNCI A TSAKANINSU (tun daga nan duniya) ." Yace :


" Da ba don Allah ya riga ya qaddara haka ta kasance cikin qaddara ta farko ba, haqiqa da Ya yi hukunci tsakaninsu a yayin da suka rarraba, kuma ya halakar dasu ba tare da Ya jinkirta musu ba. Sai dai ya jinkirta musu ne zuwa wani ajali ambatacce da aka qaddara. Kuma lalle wadanda suka gaji littafi a bayansu suna cikin kokonto daga gare shi mai sanya wasiwasi (doubt). Wannan kinaya ce daga wadanda suka warware al'amarin Manzon Allah (S. A. W. W) (na wilayar shugaban muminai Imam Ali (A. S). 


المصدر :  بحارالأنوار، ج9، ص234 


- تفسير أهل البيت عليهم السلام ج13، ص590


Wannan rabuwar da aka samu ita ce, wasu su kayi tawaye wasu kuma suka sallama al'amarinsu wajen bin abinda Allah da ManzonSa ya bar musu. Sai aka qirqiro Mazhabobi da ra'ayoyi don kare abinda ake kai na son zuciya. 


Wannan kuwa ya cigaba da tafiya har zuwa yau daidai lokacin da nake wannan rubutu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


29th January, 2023/ 8th Rajab, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post