CIKAKKEN RAHOTON ABUN DAYA FARU A ABUJA YAU ALHAMIS 30/3/2023.

 


Kamar yadda aka sani, yaune ranan da alkali zai yanke Hukunci akan Fasfo din Jagora Sayyid Zakzaky (H) da Mai Dakinsa Malama Zeenah Ibrahim. Da Musalin karfe tara 9:00 na safiyar yau din, `yan'uwan sunyi Cincirodo a bakin Federal High Court inda ake Shari'ar, suna Kira da'ayiwa Jagora (H) da Mai dakinsa Malama Zeenatuddin Ibraheem Adalci.



Bayan fitowar Lauyoyin Jagora Sayyid Zakzaky (H) sunyi bayanin Yadda zaman ya Kasance, inda Shi Alkali yace ba Wani hujja da aka kawo mishi na kin bada Passport din, abun da muka sani dae shi Alkali bai ce a bada Fasfo ba, Zakuji Sauran rahoton kotun daga su Lauyoyin Sheikh Zakzaky (H) din.


Biyo bayan Bay


anin Lauyan Malam (H) sai Matasan dake bakin Kotun, suka Fara kabbara, Nan take suka hau kan kwalta suka fara Muzahara Cikin Izza suna Kira da'a saki Fasfo din Jagora (H).


Muzaharar ta taso daga bakin Kotun inda ta ratsa ta iso har federal Secretarial, Muzahara tana tafiya Cikin lafiya akaje aka yiyo kwana da. Muzaharar aka Kara tinkarowa Federal Secretarial, Muzaharar ta iso Junction sai ga rundunar Jami'an tsaron Nijeriya, suka afkawa 'yan uwa da tiyagas, biyo bayan tiyagas din da suka harba 'yan uwan sun tinkaresu da kabbara, kawai sai suka Fara amfani da harsasai masu Rai, Nan take sukai ta Harbin 'yan uwa Babu kakkautawa, 


Zuwa yanzu hada wannan rahoton babu Shahidi ko Daya da aka samu a Waki'ar kokuma Labarin wani Dan Uwa Wanda aka Kama, ammah akwai 'yan uwan da aka harba da Dama,masu (rauni) kenan.


Isa Charis ✍️

Ali-assajad ibn taheer

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Ubangiji ya saka mana wannan zalincin da ake mana da gaggawa, yabaiwa su sayyed lafiya

    ReplyDelete
Previous Post Next Post