HAQIQANIN MA'ANAR AZUMI !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BARIN CI DA SHA DA JIMA'I BA SHINE AZUMI BA
Al-Qur'ani mai tsarki ya hane mu da ci, sha da kuma jima'i cikin dukkan yinin kwanakin watan Ramadana, amma ba ana nufin barin wadannan shine azumi ba.
Sau da yawa mutum zai iya nisantar wadannan abubuwa uku cikin yinin kwanakin azumi amma a qarshe ya tashi ba cikin wadanda su kayi azumi ba, wato ba cikin masu samun ladan azumin ba.
Ya zo cikin riwayoyi kamar haka :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
كِتَابُ الْغَارَاتِ، لِإِبْرَاهِيمَ بْنِ مُحَمَّدٍ الثَّقَفِيِّ بِإِسْنَادِهِ عَنِ ابْنِ نُبَاتَةَ قَالَ: قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع فِي بَعْضِ خُطَبِهِ :
" الصِّيَامُ اجْتِنَابُ الْمَحَارِمِ كَمَا يَمْتَنِعُ الرَّجُلُ مِنَ الطَّعَامِ وَ الشَّرَابِ."
Cikin Kitabul-Ghaaraati, na Ibrahim Bn Muhammad Ath-Thaqafiy, da isnadinsa daga Ibn Nubatata yace : Amirul-muminina (A. S) ya fada cikin sashen Khudubobinsa :
" AZUMI SHINE NISANTAR ABUBUWAN DA AKA HARAMTA KAMAR YADDA MUTUM KE HANUWA DAGA ABINCI DA ABIN SHA. "
نهج البلاغة تحت الرقم 145 من قسم الحكم.
Barin cin abinci da abin sha na daga cikin abinda mai azumi ke nisanta masu nuna cewa yana azumi . Saboda haka kamar yadda ya kasance yana nisantar wadannan abubuwa haka ake so ya nisanci dukkan abubuwan da aka haramta, domin rashin nisantar abubuwan da Allah ya haramta kan bata azumi. Wannan dalili yasa Manzon Allah (S. A. W. W) yayi nuni cikin wani hadisi da cewa masu yawa daga cikin masu azumi basu da ladan komai na barin ci da sha nasu face yunwa da qishirwar banza . Hakama sallar tarawihi, babu ladan sallar gare su face wahalar banza.
مَجَالِسُ الشَّيْخِ، عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ عُبَيْدِ اللَّهِ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عِيسَى عَنْ عَلِيِّ بْنِ مَهْزِيَارَ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ سَعِيدٍ عَنِ النَّضْرِ بْنِ سُوَيْدٍ عَنِ الْقَاسِمِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ جَرَّاحٍ الْمَدَائِنِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ الصِّيَامَ لَيْسَ مِنَ الطَّعَامِ وَ الشَّرَابِ وَحْدَهُ ثُمَّ قَالَ قَالَتْ مَرْيَمُ إِنِّي نَذَرْتُ لِلرَّحْمنِ صَوْماً أَيْ صَمْتاً فَإِذَا صُمْتُمْ فَاحْفَظُوا أَلْسِنَتَكُمْ وَ غُضُّوا أَبْصَارَكُمْ وَ لَا تَنَازَعُوا وَ لَا تَحْسُدُوا قَالَ وَ سَمِعَ رَسُولُ اللَّهِ ص امْرَأَةً تُسَابُّ جَارِيَةً لَهَا وَ هِيَ صَائِمَةٌ فَدَعَا بِطَعَامٍ وَ قَالَ لَهَا كُلِي قَالَتْ إِنِّي صَائِمَةٌ فَقَالَ كَيْفَ تَكُونِينَ صَائِمَةً وَ قَدْ سَبَبْتِ جَارِيَتَكِ إِنَّ الصَّوْمَ لَيْسَ مِنَ الطَّعَامِ وَ الشَّرَابِ."
Ya zo cikin Majaalisi na Sheikhi, daga Hussaini Bn Ubaidullahi, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Yahya, daga babansa daga Ahmad Bn Muhammad Bn Isah, daga Aliyu Bn Mahziyaara, daga Hassan Bn Sa'eed, daga Nadhri Bn Suwaidi, daga Qaseem Bn Sulaimana, daga Jarraahil-Madaa'iniy, daga Abu Abdullah (A. S) yace :
" LALLE SHI AZUMI BA WAI (barin) ABINCI DA ABIN SHA BANE KADAI. " Sa'annan yace :
" MARYAMA TA CE : " LALLE NI NA YI BAKANCEN AZUMI GA MAI RAHMA." MA'ANA YIN SHIRU, IDAN KUNA AZUMI KU TSARE HARSUNANKU 😜 KUMA KU RINTSE IDANUWANKU 👀. KUMA KADA KUYI JAYAYYA, KADA KUYI HASSADA. " Yace : " MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA JI WATA MATA NA ZAGIN KUYANGARTA (Baiwarta) ALHALI TANA AZUMI. SAI YAYI KIRA AKA ZO MASA DA ABINCI YACE MATA :
" KI CI. " Tace :
" Ai ni ina azumi. " SAI YACE :
" TA YAYA ZA KI KASANCE MAI AZUMI ALHALI KIN ZAGI KUYANGARKI ? AI SHI AZUMI BA WAI BARIN CIN ABINCI NE DA SHA BA. "
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج93، ص: 295
Saboda haka sai mu kasance masu nisantar abubuwan da aka haramta mana don samun ingancin azumin mu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th March, 2023/ 2nd Ramadan, 1444.