MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KOWA NA GANI KAMAR SHINE JAGORAN KANSA
Ga wanda yasan wanene Manzon Allah (S. A W. W) kuma yasan koyarwarsa da abinda yabar mana dole yayi mamaki idan ya kalli yadda al'ummarsa ke ciki a halin yanzu.
Bari muyi amfani da kalaman Imam Ali (A. S) Kai-tsaye don gudun tsawaitawa.
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
Imam Ali (A. S) yace :
" فَيَا عَجَبَا وَمَا لِي لَا أَعْجَبُ مِنْ خَطَإِ هَذِهِ الْأُمَّةِ عَلَى اخْتِلَافِ حُجَجِهَا فِي دِيَانَاتِهَا لَا يَقْتَصُّونَ أَثَرَ نَبِيٍّ وَلَا يَقْتَدُونَ بِعَمَلِ وَصِيٍّ وَلَا يُؤْمِنُونَ بِغَيْبٍ وَلَا يَعْفُونَ عَنْ عَيْبٍ يَعْمَلُونَ فِي الشُّبُهَاتِ وَيَسِيرُونَ فِي الشَّهَوَاتِ الْمَعْرُوفُ فِيهِمْ مَا عَرَفُوا وَالْمُنْكَرُ عِنْدَهُمْ مَا أَنْكَرُوا مَفْزَعُهُمْ فِي الْمُعْضِلَاتِ إِلَى أَنْفُسِهِمْ وَتَعْوِيلُهُمْ فِي الْمُبْهَمَاتِ عَلَى آرَائِهِمْ [رَأْيِهِمْ] كَأَنَّ كُلًّا مِنْهُمْ إِمَامُ نَفْسِهِ قَدْ أَخَذَ فِيمَا يَرَى بِغَيْرِ وَثِيقَاتٍ بَيِّنَاتٍ وَلَا أَسْبَابٍ مُحْكَمَاتٍ."
" ABIN MAMAKI ! TA YAYA KUWA BA ZANYI MAMAKI BA DAGA KURA-KURAN WANNAN AL'UMMA AKAN SASSABA HUJJOJINTA CIKIN ADDININTA . BA SA BIBIYAR TAFARKIN ANNABI KUMA BA SA KOYI DA AL'AMARIN WASIYYI, KUMA BA SA IMANI DA GHAIBU KUMA BA SA YIN AFUWA GAME DA AIBU.
SUNA AIKI CIKIN SHIBUHOHI, KUMA SUNA CIGABA (da aikinsu) CIKIN ABINDA ZUKATANSU KE SO. SANANNEN ABU A CIKINSU BASU SAN SHI BA, ABINDA YA KAMATA SU QI SHI (suyi inkarinsa) BA SA QINSA. DAMUWARSU KAWAI ITA CE MASLAHAR KANSU, TAWILINSU SHINE ZARTAR DA HUKUNCI AKAN RA'AYINSU (ba bisa hukuncin Allah da Manzonsa ba), KAMAR DAI KOWANNE DAGA CIKINSU SHINE JAGORAN KANSA. KAWAI YA RIQI ABINDA YAKE GANI NA RA'AYINSA SHINE DAIDAI BA TARE DA HUJJA BAYYANANNIYA KO KUMA WANI DALILI NA HUKUNCIN (Shari'a) BA. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
29th January, 2023/ 8th Rajab, 1444.