MATSAYIN YIN ALWALA CIKIN WANKAN JANABA !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Idan kana karanta littafan fiqhu na Sunnah za kaga suna sharadanta yin alwala ciki ko bayan wankan Janaba don yin sallah.
Wasu suka ce ana yin alwala cikin wankan, amma kuma a kiyaye shafar Azzakari don kada a warware alwalar. Wasu kuma suka ce ana iya jinkirta yin alwalar zuwa qarshen wanka.
Ma'ana dai yin alwala na daga cikin sharadin wanka, sai dai an bada zabi nayi cikin wankan ko kuma jinkirtawa zuwa bayan wankan.
To, amma cikin shari'ar muslimci a aya ko hadisi babu batun wannan alwala, wanka kawai ake yi yayin janaba, kuma ya wadatar maka da yin komai na ibada.
Ya zo cikin aya da hadisi cewa;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
" يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قُمۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغۡسِلُواْ وُجُوهَكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ إِلَى ٱلۡمَرَافِقِ وَٱمۡسَحُواْ بِرُءُوسِكُمۡ وَأَرۡجُلَكُمۡ إِلَى ٱلۡكَعۡبَيۡنِۚ وَإِن كُنتُمۡ جُنُبٗا فَٱطَّهَّرُواْۚ......"
" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! IDAN KUKA TASHI ZUWA GA SALLAH KU WANKE FUSKOKINKU DA HANNAYENKU ZUWA MURAFIQAI, KUMA KU SHAFI SASHEN KAYUKANKU DA QAFAFUNKU ZUWA KA'AB. IDAN KUMA KUNA HALIN JANABA, TO, KUYI WANKA......."
(SURATUL-MA'IDA, AYA TA 5)
Idan muka kalli siyaqin wannan aya za muga cewa tana nuna mana sharadin yin alwala ne yayin da muka tashi zuwa ga sallah, wato wajibi ne yin alwala kafin yin sallah.
Sai kuma aka fayyace mana cewa idan kuma za muyi sallah alhali muna da janaba, to, maimakon yin alwala sai dai kawai muyi wanka .
Idan kuma muka koma cikin hadisi za muga yadda hadisin ya qara bayyanar mana da cewa ba a yin alwala bayan wanka. Ga riwayar nan cikin BABIN TAIMAMA cikin Sunan na Nisa'i.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
باب تَرْكِ الْوُضُوءِ بَعْدَ الْغُسْلِ:
433- أَخْبَرَنَا أَحْمَدُ بْنُ عُثْمَانَ بْنِ حَكِيمٍ قَالَ: حَدَّثَنَا أَبِي حَدَّثَنَا حَسَنٌ عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ (ح) وَأَنْبَأَنَا عَمْرُو بْنُ عَلِيٍّ قَالَ: حَدَّثَنَا عَبْدُ الرَّحْمَنِ قَالَ: حَدَّثَنَا شَرِيكٌ عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ عَنِ الأَسْوَدِ عَنْ عَائِشَةَ قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ يَتَوَضَّأُ بَعْدَ الْغُسْلِ.
Ahmad Bn Usmana Bn Hakeem ya bamu labari yace: Babana ya bamu labari, Hassan ya bamu labari daga baban Ishaq, kuma Amruu Bn Aliyu ya bamu labari yace: Abdurrahman ya bamu labari yace: Shareeku ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Aswadi, daga A'ishata tace:
" MANZON ALLAH (S.A.W.W) YA KASANCE BA YA YIN ALWALA BAYAN WANKA."
(Sunan-Nisa'i, Babin barin alwala bayan wanka, hadisi, hadisi mai lamba 433).
To, yanzu da wacce hujja suka dogara na sanya alwala cikin sharadin wankan janaba ?
Yanzu idan mutum yayi alwala a wankan janaba bai sabawa umarnin Allah da koyarwar Ma'aikinsa (S.A.W.W) ba ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
31st July, 2021/ 21st ga Zul-Hijjah, 1442.