MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Wanda Tafiye-tafiye ne sana'arsa kamar Direban mota ko wanda ya aikinsa ya dogara da yin tafiye-tafiye wajibi ne suyi Azumi , amma idan ya zama sunyi tafiya ta daban wacce bata shafi aikinsu ba to anan dole suyi ƙasaru a Sallah kuma dole su ajiye Azumi , sun zama kamar waninsu .
Ma'ana da ace wani uzuri daban da bai shafi harkarsu ta Tuƙin Mota ba zai sa suyi wata tafiya daban , kamar ziyarar ƴan uwa , to anan ba za suyi aiki da hukuncin da suke aiki dashi ba a lokacin da suke gudanar da sana'arsu ba , suma za su ɗauki kansu kamar sauran mutane ne a wannan hali na tafiya .
9/Ramdan/1444H - 21/3/2023