@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AYI HATTARA YARAN ZAMANI
Na ambaci yaran zamani ne saboda suna daga cikin jinsin wadannan mutane uku wadanda ba za su shiga Aljannah ba sakamakon rashin biyayyarsu ga mahaifansu.
Idan ka tara yaran wannan zamani ka kasa su gida goma sai ka tarar daqyar ka sami kaso biyu masu biyayya ga mahaifansu cikin kowanne irin yanayi alhali ba wai mahaifan nasu nayi musu umarni wajen sabawa Ubangiji bane.
Ba wai cikin wadanda muke kira Amawa kadai wannan matsala take ba, a'a, har cikin masu da'awar sune ke kan karantarwa Ahlul-Bait (A. S) , wato masu kiran kansu da 'yan'uwa ko 'yan Shi'ah.
Ya zo cikin riwaya daga Imam Ali (A.S) yana cewa :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" ثَلاثَةٌ لا يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ: سَفّاكُ دَمٍ حَرامٍ، وَ عاقُّ والِدَيْهِ، ومَشَّاءٌ بِنَميمَةٍ."
" (jinsin mutane) UKU BA ZA SU SHIGA ALJANNAH BA : MAI ZUBAR DA JINANE BISA HARAM, DA MAI SABAWA MAHAIFA, DA KUMA MAI YAWO DA ANNAMIMANCI (mai haddasa fitina tsakanin wani da wani). "
المصدر : عيون الحكم والمواعظ
Wadannan sune jinsin mutane uku da aka kawo cikin wannan hadisi wadanda aka ce ba za su shiga Aljannah ba.
Sai kowa yayi nazari akan kowanne daga cikinsu, amma ni dai na danyi bayani kadan kan yara masu sabawa mahaifansu, domin ita ce tafi yawa na daga abinda ake aikatawa wadanda suke yiwa mutum shamaki da Aljannah.
YAA ALLAH KA SHIRYAR MANA DA 'YA'YAYENMU WADANDA KE NEMAN SHIRIYA
🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼👇🏽🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
5th March, 2023/ 13th Sha'aban, 1444.