[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Bayan gama wannan yaki na Siffin, Imam Ali (a.s) ya kama hanyar dawowa Kufa, helkwatar gwamnatinsa. A hanyar dawowar kuwa wani abu ya faru, in da wasu jama'a kimanin 12,000 daga cikin sojojinsa suka janye daga cikin asalin ayarin suka koma gefe.
Su dai wadannan mutane suna nuna rashin amincewarsu ne da yadda lamari ya gudana a Siffin, suna cewa Imam Ali (AS) ya ha'inci Musulunci ta hanyar amincewa da wannan yarjejeniya, don haka dole ya nemi tuba a wajen Allah (waliyazu billahi), alhali kuwa su wadannan mutane su ne dai suka ajiye makamansu suka ce ba za su yi yaki ba saboda Mu'awiyya da rundunarsa sun daga Alkur'ani, duk kuwa da gargadinsu da Imam Ali (AS) din ya yi na kada su Yadda Da haka amma suka ki yarda Wadannan mutane dai su ne wadanda ake kira da Alkhawarij (Khawarijawa), wato wadanda suka tawaye ga addini.
Lokacin da sojojin Sayyidina Ali (AS) suka kusa da garin Kufa sai wadannan Khawarijawan suka yi sansani a wani kauye da ake ce ma (Harura) suna masu cewa babu wani mutum da ke da hakkin shugabanta wani mutum, dukkan mutane daya suke.
Ta hakan ne suka su ka ki amince da Imam Ali (AS) da kuma Mu'awiyya, suna masu cewa abin da kawai suka yi imani da shi shi ne La Hukma Illa Lillah wato Babu Wani Hukumci (gwamnati ko jagora) Sai Na Allah.
Ganin haka sai Imam Ali ya tura Sasa'a bn Sauhan da Ziyad bn Nazr al-Harisi tare da Ibn Abbas wajensu don tattaunawa da su, kai daga baya ma shi kansa ya je wajensu yana mai kokarin nuna musu cewa sun yi kuskuren fahimta kalma La Hukma Illa Lillah, da kuma bayyana musu cewa yarda da sulhun da ya yi bai saba wa Alkur'ani mai girma ba.
Kamar yadda kuma ya nuna musu kuskurensu wajen ajiye makamansu a lokacin yaki, abin da ya tilasta masa umartan Malik al-Ashtar ya dawo duk kuwa da nasarar da yake samu.
Har ila yau ya sake tunasar da su cewa su ne fa suka tilasta masa amincewa da yin sulhun da kuma yarda da Abu Musa al-Ash'ari a matsayin wanda zai wakilce shi a taron sulhun.
Bayan duk wannan karin bayani dai, Khawarijawan sun amince da cewar sun yi kuskure, to amma shi ma ya yi kuskure don haka dole ne ya nemi gafara.
Imam Ali (AS) ya ki amincewa da hakan yana mai cewa babu wani laifin da ya yi ballantana ya nemi gafara, haka dai aka watse ba tare da an cimma matsaya ba.
Su kuwa Kharijawa sai suka wuce suka kafa sansaninsu a wani waje da ake ce ma Nahrawan, kimanin kilomita 12 daga birnin Bagadaza, daga baya ma wasu mutane daga Basra suka iske su da shiga cikinsu.
A bangare guda kuma, bayan samun labarin yadda wannan yarjejeniya ta sulhu tsakanin Amr bn al-Aas da Abu Musa al-Ash'ari ta gudana, sai Imam Ali (AS) ya kuduri aniyar ci gaba da yakan 'yan tawayen, inda ya rubuta takarda ga Khawarijawan yana mai bayyana musu cewa lalle wannan abin da aka cimma ya saba wa Littafin Allah da kuma sunnar ManzonSa, don haka bai amince da ita ba, don haka yana kiransu da su taimaka masa wajen gamawa da 'yan tawaye.
To amma sai Khawarijawan suka rubuta masa cewar: "A'a fahimtarmu amincewar da ka yi na a tattauna tun farko bidi'a ce, don haka idan har ka amince da hakan to sai ka tuba mu kuma sai mu yi tunanin mene ne abin yi".
Wannan wasika ta su dai ta sanya Imam Ali (AS) ya fahimci cewa lalle fa lamarinsu ya yi nisa kuma batarsu ta bayyana a fili, babu wani tsammani tattare da su. Don haka sai ya yi azama tafiya Sham don yakan Mu'awiyya da sauran 'yan tawayen da suke tare da shi, inda ya yada zango a wani waje da ake kira al-Nukhaylah.
A hanyarsa ta zuwa Sham, sai labari ya zo wa Imam Ali (AS) cewa Khawarijawan sun kashe gwamnan Nahrawan din Abdullah bn Khabbab bn al-Aratt da kuma sauran wasu muminai na garin.
Don haka sai ya tura Harith bn Murrah al-Abdi don binciko gaskiyar labarin, shi ma suka kashe shi. Ganin haka sai Imam Ali (AS) ya yanke cewa lalle tawayen nasu ya kai wani matsayin da ba za a rufe ido a kansa ba da kuma cewa akwai yiyuwar su kai wa Kufa hari matukar suka san Amirul Mumininan ba ya nan. Don haka sai ya canza hanya don fuskantarsu da kuma ladabtar da su.
Koda isowarsa Nahrawan, Imam Ali (AS) ya bukaci Khawarijawan da su mika mutanen da suka zubar da jinin wadannan bayin Allah don su fuskanci hukumci, amma suka ki mika su suna masu cewa dukkansu ne suka kashe su, saboda masu sabo ne su.
Imam Ali (AS) da sojojinsa dai ba sa son yakan wadannan Batattun mutane, don haka sai Imam Ali (AS) ya aiki Abu Ayyub al-Ansari da sakon neman zaman lafiya zuwa gare su. Inda ya kiraye su zuwa ga mika su sami tsira.
Sannu a hankali sai da dama daga cikinsu, kungiya-kungiya suka fara kaucewa suna barin wannan kungiya. Daga karshe dai sai aka bar wasu mutane kimanin 1,800 daga cikin Khawarijawan masu tsattsauran ra'ayi suka ki mika wuya suna masu shirin yakan halifan zamaninsu.
Amirul Muminina Ali (AS) Yace
"Ina gargadinku da cewa za a kashe ku a wannan guri, alhali kuwa ba ku da wani uzuri gaba ga Allah ko kuma wata hujja ba. Kun fito daga gidajenku kana kaddarar Ubangiji ta ritsa da ku. Tun farko na gargade ku dangane da wannan tattaunawa ta zaman lafiya, amma kuka yi watsi da wannan shawara tawa har sai da kuka tilasta min yarda da abin da kuke so. Ku mutane ne da kuke wasa hikima da wayo. Kaiconku! ban sanya ku cikin wani bala'i ba kamar yadda kuma ban nufe ku da wata cutarwa ba".
Daga nan sai Khawarijawan suka kai hari mai girman gaske kan sojojin Ali (AS), amma ina ba za su iya da wadannan jaruman sojoji ba, nan ba da jimawa ba aka kashe su dukkansu, face dai wasu mutane tara kawai da suka tsira suka gudu zuwa Basra da sauran garuruwa. A can din ma dai ba su tuba ba inda suka je suka ci gaba da yada kararraki da kiyayya da Ali (AS) tsakanin mutane da kuma sake tara magoya baya.
Wannan yaki dai na Nahrawan dai ya faru ne a ran 9 ga watan Safar shekara ta 38 bayan hijira. Shekara biyu kuma bayan haka, wadannan Khawarijawa suka tsara da tura wadansu mutane uku daga cikinsu da nufin kashe Imam Ali (AS), Da Mu'awiyya da kuma Amr bn al-Aas, suna masu cewa su ne tushen barna da fitinar da ke gudana. Daga karshe dai sun sami nasarar kashe Ali (AS), amma Mu'awiyya da Ibn al-Aas sun tsira.
Ta haka ne dai aka kawo karshen wannan yaki, Ali (AS) ya komo gida, ya bar shirin da ya faro na kai wa Sham hari, shirin da bai sake samun damar yinsa ba har lokacin da ya yi shahada.