[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Daga Nuruddeen Isyaku Daza
Dan majalisar dokoki na yankin mazabar Bosso a jihar Neja kuma shugaban kwmitin kwadago na majalisar, Malik Madaki Bosso ya yi kira ga majalisar kasa da ta gggauta daukar matakin fuskantar gwamnatin tarayya gadan-gadan akan sabon tsarin canjin kudi.
Malik Madaki ya ce manufar gwamnati shine tsare dukiyoyi da rayukan al'umma tare da sama masu walwala, kuma duk wadannan matakan babu wacce gwamnatin Buhari ba ta gaza ba.
Dan Majalisar wanda dan jam'iyyar APC ne, ya ce ba daidai bane a ce Gwamnatin su da talakawa suka bada gudunmuwar kafa ta a ce yau sune suke shan wahala a cikin ta, don haka ya bukaci majalisar kasa da ta dauki matakin da ya dace kan lamarin koda kuwa zai kai ga tsige Shugaban Kasa Buhari ne.
Shin kuna tare dabshi akan wannan ra'ayin nashi?