[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Nasir Isa Ali
Ranar Asabar 28/1/2023 ne Shaikh Dr. Sunusi Abdulkadir Koki ya kintsa domin kama hanyar tafiya zuwa Katsina domin halartar MU'UTAMAR AMM' wacce aka shirya aka kuma kammala a garin na Katsina. Sai kuma ga sako daga babban malamin addinin musuluncin nan dake garin Maiduguri waton Shaikh Shareef Ibrahim Saleh na cewar zai gana da shi Dr. Sunusi din a ranar Lahadi 29/1/2023.
Don haka sai Dr. Sunusi ya hakura da tafiyarsa ta zuwa Katsina din domin ya samu damar ganawa da wannan babban malamin addinin musulunci.
Ranar Lahadi 29/1/2023 sai shaikh Dr. Sunusi da masu yi masa rakiya suka isa gidan hamshakin malamin dake Zone 2 Lungu Close, Abuja, domin gabatar da wannan ziyarar mai matukar muhimmancin gaske.
Bayan sun gaisa da kuma gabatar da kai ga shaikh Ibrahim Saleh, sai Dr. Sunusi ya fara da bayyana wa malamin maqasudin ziyarar tasu da cewar, sun kawo masa ziyara ne domin karfafa zumunci, kusantar juna, girmama malamai da kuma samun hadin kan musulmi baki daya.
Shaikh Dr. Sunusi ya bayyana masa yadda alummar musulmi suke matukar karuwa da wa'azi da jawabansa mai cike da kaunar annabi da iyalan gidansa tsarkaka. Haka zalika sun kawo masa ziyara ne domin girmamawa da kuma neman addu'ar sa mai albarka da kuma tabarrukinsa a matsayinsa na shareefi jikan manzon Allah (saww)
Dr.Sunusi ya kara bayyana wa malamin yadda shaikh Zakzaky ya kwashe tsawon shekaru yana da'awar a koma ga Allah ta'ala, da kuma yadda shaikh Zakzaky ya dukufa wajen yin aiki tukuru da kuma kira zuwa ga hadin kan musulmi. Wannan ziyarar da muke kai wa maluman musulunci da sauran al'umma na daya daga cikin tarbiyar da shaikh Zakzaky ya koya wa mu almajiransa inji Dr. Sunusi.
A karshen jawabinsa, Dr.Sunusi ya bayyana masa halin da lafiyar shaikh Zakzaky da iyalinsa ke ciki da kuma yadda aka hana su Fasfo domin fita waje neman lafiyarsu.
A nasa jawabin shaikh Shareef Saleh ya bayyana matukar jin dadinsa da farin ciki bisa wannan ziyara ta zumunci da girmamawa da kuma neman maslaha da hadin kan musulmi.
Shaikh ya bayyana cewar "duk da mu ahlul sunnah ne amma muna matukar kaunar ahlulbaiti sosai da sosai, sannan bama gaba da masoyan ahlulbaiti (as) Yace tabbas abubuwa marasa dadi sun faru a tarihin musulunci, amma du da haka ya zama wajibi musulmi su hada kansu domin yin biyayya ga Allah.
Shaikh Shareef Ibrahim Saleh ya kara Jan hankali da cewar lallai a dage wajen cigaba da neman hadin kan musulmi, domin yin hakan bin umurnin Allah ta'ala ne.
A karshe shaikh Ibrahim Saleh ya kara tambayar halin da lafiyar shaikh Zakzaky da iyalinsa ke ciki? A karshe shikh Shareef Ibrahim Saleh ya mika sakon gaisuwarsa ďa kuma fatan alhrinsa zuwa ga jagoran harkar musulunci a Nijeriya shaikh Ibrahim Zakzaky (H)
A cikin masu yiwa Dr.Sunusi rakiya akwai:
Dr. Yusha'u Abuja
Alh. Abdukarim karmajiji
Lawan Muhammad Kano
Kabiru Abubakar Kano
----------
Nasir Abu Nusaiba Muhammad