[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
1. Wato na yarda hundred percent da tãken da ake faɗa ma (JALLABAR HAUSA) wato (KANO KO DA ME KA ZO AN FI KA).
Wannan tãke ya samo asali ne saboda garin Kano gari ne da ya tattara dukkan nau'ukan mutane da ake buƙata a rayuwa da ma waɗanda fitina ne a rayuwa.
Wai hukuncin kisa ne aka yanke ma Dr. Abduljabbar (H) amma babu Allah ya ce, babu Annabi ya ce a hukuncin. An yi amfani ne da wani Larabci na Alƙali Iyãd wanda bai wuce saɗara ukku ko huɗu ba.
Kuma abin damuwa, shi kansa Larabcin da aka karanta aka yi hukuncin da shi, malamai tun tale - tale sun yi fakkin maganar.
Wato sun faɗi cewa wanda ya furta wata kalma ga Annabi (saw) alhali ba yana mai yarda da ita ba, korewa ma yake yi, to sam babu kisa a kansa.
Sai de malamai da ɗalibai da yawa a wannan zamani namu bã su bincike mai zurfi a ilmai na addini, basu san daraja da ƙimar binciken ba, sannan basu san me ake kafa hujja da shi ba, shi yasa aka karanto masu wasu ƴan saɗarori a littafin Asshifā aka ce an yanke hukuncin kisa ga Musulmi Masoyin Annabi (saw).
______
Ga Larabcin da Sarki Yola ya karanto daga littafin Asshifã 👇 :
وَإِنِ اتُّهِمَ هذا الحاكي فيما حكاه أنه اخْتَلَقَه ونسبه إلى غيره ، أو كانت تلك عادة له ، أو ظهر استحسانه لذلك ، أو كان مولعًا بمثله ، والاستخفاف له ، أو التحفظ لمثله ، وطلبه ورواية أشعار هجوه صلى الله عليه وسلم وسبه . فحكم هذا حكم الساب نفسه ، يؤاخذ بقوله ، ولا تنفعه نسبته إلى غيره ، فيبادر بقتله ، ويعجل إلى الهاوية أمه
______
2. Wannan magana da ta gabata (Sarki Yola) cewa ya yi wai maganar Imam Malik ce Alƙadi Iyad ya kawo. Ko ta yaya wannan magana ta zama ta Imam Malik (rh)?.
Babu ko shakka jin haka daga gare shi abin damuwa ne matuƙa. Kuma alama ce da ke nuna rashin ƙwarewa da cancantarsa a fannin Shari'a da aka ɗora shi. Lallai (Abul Hasanil Fãliy) ya gasgata da yace :
تَصَدَّر للـتــَّـدْريس كلُّ مُـهـوَّسٍ ☆ بَـلـيـدٍ تَـسـمَّى بـالفقيهِ الـمُـدَرِّسِ
فَحُقَّ لأهـل الـعلم أن يَـتـمـثَّلـوا ☆ بِبَيْتٍ قديمٍ شاع في كلِّ مَجْـلِسِ
لـقــد هُــزِلَــتْ حتى بدا من هُزالِها ☆ كُلاها وحَتَّى سامَها كلُّ مُفْلِسِ
______
(3) Alkhafãjiy malami ne da ya shahara kuma ya yi fice saboda bakandamen sharhinsa ga littafin Asshifã wato :
نسيم الرياض في شرح شفاء القاضي عياض
A cikin waɗanda suka sharhanci littafin Asshifã wannan sharhi a yanzu de kam babu tamkarsa. Idan ka duba mujallad na 6 shafi na 255 za kaga Khafãjiy ya sharhanci wannan magana ta Alƙadi Iyad da Sarki Yola ya kawo. Ga sharhin kamar haka 👇 :
وَإِنِ اتُّهِمَ هذا الحاكي فيما حكاه أنه اخْتَلَقَه) ، أى اخترعه ولم يقله غيره فيُحْكَى عنه وهو يعتقده (ونسبه إلى غيره) بحكايته عنه خوفاً من المؤاخذة به (أو كانت تلك عادة له) بأن يكثر من ذكره ويزعم أنه حاك له (أو ظهر) حال نقله (استحسانه لذلك) وأنه لا محظور فيه (أو كان مولعًا بمثله) بفتح اللام اسم مفعول ، الولع بالشىء الإكثار منه مع إظهار الميل له وأنه يحبه (والاستخفاف له)، أى عده هينًا عنده لا محذور فيه (أو التحفظ) أى حفظه كثيرًا (لمثله) مما هو قبيح كريه (أو طلبه) ممن يعرفه حرصًا عليه (و) كثرة (رواية أشعار هجوه صلى الله عليه وسلم) الذي هجاه به المشركون مما ذكره أهل السير (وسبه) المنقول عن المشركين
(فحكم هذا) الحاكي (حكم الساب) من غير حكاية له (نفسه) لا حكم الحاكي وحكمه أنه (يؤاخذ بقوله) مما يستحقه الساب (ولا تنفعه نسبته) لقوله ما حكاه (فيبادر بقتله) كالساب
قال ابن حجر : وما ذكره من المبادرة بقتله ، أى إن لم يتب
______
4. Idan mai karatu ya dubi wannan sharhi na Khafãjiy ze ga tun farko ya rosa hukuncin da Alƙali Sarki Yola ya zartas. Saboda faɗinsa :
أى اخترعه ولم يقله غيره فيُحْكَى عنه وهو يعتقده
Anan Khafajiy yana so ya faɗa maka shi wanda ya furta wata kalma a janãbin Annabi (saw) za a duba ne a ga shin ya yi Imani da abinda ya furta akan Annabi (saw) ko kuwa bai yi Imani da shi ba.
Idan wanda ya faɗa ma Annabi (saw) wannan kalma shima bai yarda da tabbatuwarta akan Annabi (saw) ba, ma'ana bai yi Imani da ita ba korewa yake yi, to babu maganar kisa a kansa ko da kuwa shi ya ƙirƙiri kalmar.
Faɗin Khafãjiy da yace (وهو يعتقده) ya warware komai tunda yana nufin sai wanda ya yi imani da tabbatuwar abinda ya faɗa akan Annabi (saw).
TO BALLANTANA CIKAKKEN MASOYI DA YA FURTA WATA KALMA DAN FITO DA WATA ƁARNA DA AKA ƘUDUNDUNE AKA YI MATA KWALLIYA A CIKIN LITTAFAI.
______
5. Bugu da ƙari, me karatu ze ga Khafãjiy ya naƙalto sharhin da (Ibnu Hajar Alhaitamiy Almakkiy) ya yi ma Alƙadi Iyad.
A gurin Ibnu Hajar ko shi wanda ya ƙirƙiri wata kalma akan Annabi (saw), kuma ya yi imani da tabbatuwarta a kan Annabi (saw), ma'ana shi ba korewa yake yi ba, to ba za a kashe shi ba idan dai ya tuba. Wato faɗinsa :
قال ابن حجر : وما ذكره من المبادرة بقتله ، أى إن لم يتب
TO INÃ GA WANDA YÃ FAƊI KALMAR NE DAN YA BADA KARIYA GA JANABIN ANNABI (SAW).
______
A taƙaice, rashin cancanta da karambani ya sa Sarki Yola ya karanto wancan Larabci na Alƙadi Iyad sannan ya yanke hukuncin kisa da shi. Yana da kyau Alƙalai su sani cewa lallai Alƙalanci yana buƙatar karatu na gaske da natsuwa ta kwakwalwa.
Ka kiyayi zubar da jinin mutumin da yake kallon Gabas yana Sujuda ga mahalliccinsa alhali ba kada cikakken sani da bincike akan aiwatar da hukuncin.
ادرءوا الحدود بالشبهات ، ادفعوا القتل عن المسلمين ما استطعتم
Ƙaramin Ɗalibin Dr. Abduljabbar Nasir Kabara Hafizahullah, Almajiri Saifuljabbar.