Yaumuz-Zahara(A's) Ranar Mata Ta Duniya...!!!


 

[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 



Kyautatawa abu ne mai kyau a tsakanin ma'aurata, yan uwa, masoya, brothers ga YAUMU ZAHRA tazo ranar mata ta duniya, shin me kuka tanada ko kuka shirya na farantawa sisters a wannan rana mai Albarka na farin ciki da murna na samuwar Fatima Bint Muhammad (S). 


Lalai a matsayin ka na brother yana da kyau kayi shiri na musamman domin farantawa sisters a shagwaɓa su, domin ranar ta su ce, ka samu na wani kyauta musamman kayi wa sistern ka, mata, ƙanwa, budurwa domin ranar ta mu ce, ko da baka taɓa yi wa sisternka kyauta ba, ka daure alfarman Sayyida Zahara ka mata wani kyauta wanda zai sata farin ciki da murna wanda ba zata taɓa mantawa da shi ba, dan Allah brothers kada ku bar sisters ɗin ku hakanan ba tare da kunyi musu wani kyauta ba, kun dai san Allah yana son masu kyautatawa kuma kyauta yana ƙara danƙon soyayya musamman ma ya kasance an yi saboda ɗiyar Manzon Allah (S). 


Wasu sisters ɗin sun fi so a basu kuɗi su siya abu da kansu, kamar dai ni ina san kyautan bazata ina so a kawo min kyautar abu, wasu kuma basa buƙatar a basu kuɗi, sun fi so a siyo musu wani abu na musamman a kawo musu, kamar irin kyauta na ba zata haka, zaka iya ɗinkawa sisternka hijabai ka siya mata safa da wasu abubuwan, ko kuma ka chanza mata waya ko siya mata jika da takalma, ko agogo turare kayan make up, ko irin Abays haka da dai sauran abubuwa dayawa, duk abinda kake da hali kuma Allah ya hore maka zaka iya yi mata domin faranta ranta a ranar MATA NA DUNIYA!


Na dawo gare ku Sisters, shi fa kyautatawa ga masoyi ba iya na ɓangare ɗaya bane kawai, kema a matsayin ki na sister ki yi ƙoƙari kiga kin bawa brothern ki kyauta na musamman domin farin cikin samuwar Sayyida Zahara (A.S), kuma shi kyauta na maulud ɗin Sayyida, ba sai iya mata da miji, budurwa, ƙanwa da yaya bane, zaka iya yi wa mahaifiyar ka kyauta ko yayar ka ko ai wasu na sisters haka musamman ma masu suna FATIMA!.


Allah ya hore ya buɗa hanyoyin samu, da Arziƙi mai Albarka. 


__Mujarheedah Bintu basheer

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post