Yan Uwa A Kafar Sadarwa (Social Media) !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Ya kamata mu fahimci aikin da ke gabanmu ya fi karfin tsayawa jayayya da juna, musayar baƙaƙen maganganu, aibatawa ko sukan juna (Ko da yake mun san mafi yawan masu yin hakan ba yan uwa bane, ana shiga rigarmu ne).


Ko daga fitowar Jagoranmu (H) ya gana da mutane daban-daban wadanda aka bayyana su sun fi sau 60, kuma a kowacce ganawa da yake da yan uwa ko wasu al'umma daban, ya kan yi wasu bayanan da idan su kadai muka rike a matsayin abin isarwa, sun ishe mu da al'ummar da muke ciki zama shiriya.


Ballantana kuma kowace ganawa za ka samu akwai wani bayani na musamman da ya sha bamban da na baya, ko ya zama karin bayani ko haske ne shi, wanda mutane suna kishin ruwan jin irinsu, ji irin na naci - wato wanda za a yi ta maimaita musu jin tun basu so har su karba.


Mu tambayi kawukanmu; Izuwa wane Miƙidari ne muka isar da sakonnin Jagora (H) wanda shine hakikanin sakon wannan addinin a wannan kafar da muka samu damarsa bisa yarjewar Allah Ta'ala?


Izuwa wane matsayi ne muka dabbaka umurninsa a zantukansa da yake yawan maimaita mana, na cewa mu zama masu nizami da tsayuwa kyam a tafarkin Allah, mu nesanci zagi ko mai da zagin daga masu yi ko da sun yi? Zagi ba fa yana nufin sai an ce "Uban wane" bane, hatta sukan juna da munana na nufin zagi ne, haka ma aibatawa da kokarin muzanta wani bawa cikin bayin Allah.


Ashe Jagora (H) bai ce mana mu yi kokarin kiyaye hakan har ya zama idan aka ji wani na zagi za a gane ba daga cikinmu yake ba? A wani wajen ma ya jingina masu zage-zage da soke-soken Malamai da Jahiliyya da yaransu? Har ma Jagora ya bamu wani daga siffarsu, cewa su kan bude Accounts da sunaye daban-daban da ba nasu na asali ba don wannan, manufarsu kawai shine hana yan uwa zaman lafiya?


A gabana, sau uku Jagora (H) na nuna tsananin takaici a kan yadda 'yan uwa muke mu'amalantar juna a social media da rashin kan-gado. Har na kan ji kamar na nutse a kasa saboda kunya. Wani lokaci ma na ji kamar na dena gaba daya, sai rauni ya sa na cigaba. Amma shin ba kofar gyarawa ne a garemu?


Mene ne manufar Da'awar Jagora (H)? Ina ce kira ne zuwa ga yunkurin tabbatar addini? Babban burin Harka Islamiyya shine addini ya kafu daram a kasar nan, ya zama shi ne ke da iko. A kan wannan Jagora (H) suke cewa duk wanda yake da ra'ayin ko da a zuciyarsa ce kan cewa addini ya dawo da iko birbishin komai, to ko bai shigo cikinmu ba muna ganinsa a matsayin bangarenmu ne. Yace sai dai za a iya kiransa da 'passive member' a yayin da mu ke dan taɓuka kokarin ganin hakan ya tabbata za a iya ce sunanmu 'active'.


Kuma ikon addinin nan, Jagora (H) sun fada mana me suke nufi da tabbatar addini, shine a wayi gari Addinin Musulunci da dokokinsa su zama su ne a sama. Ya zama babu wani doka ko iko a sama da zai iya karya dokar Allah Ta'ala. Idan aka samu haka shine ma'anar tabbatan addini. Kuma wannan mai yiwuwa ne sosai, har makiya sun san zai iya yiwuwa shi yasa ma suke dirarwa Da'awar da ke kira ga hakan. Da sun san ba zai yiwu ba, da za su zura ido ne kawai su kalle shi, kamar yadda za ka zurawa mutumin da yace zai zunguro tauraro ya fado kasa ido. 


Abin da nake kokarin cewa, mene ne kiran nan da Jagora (H) ya shafe shekaru kimanin 45 yana yinsa? Ya kamata mu 'yan Media mu fahimce shi sosai. Bayan mun fahimta, sai ya zama babban aikin da za mu ba kawukanmu a wannan kafar shine isar da shi a salon da mutanen da muke tare da su za su fahimce shi, akalla ko da ba su zo an yi da su ba, ya zama ba su jahilci mene ne ba.


Idan muka koma muka shagaltu da kawukanmu da soke-soken juna, da kokarin koran wasunmu daga inuwar Da'awar, muka kuma ba makiya dama suka rika bude 'Account' da sunaye daban-daban suna zage-zage, zarge-zarge, habaice-habaice, da tsine-tsine da sharrance-sharrance duk da sunan Harkar Musulunci ga wasu, to fa mun ci amanar Sahibul Asr Waz Zaman (AJ) ne, saboda mun ma tafarkinsa saddu, domin za mu hana wasu su ma fahimce mu balle su kasance tare da mu.


Social Media wata dama ce da Allah Ya bamu da ya kamata mu yi amfani da shi wajen ilmantar da kawukanmu da ilimomin addini da wanda ake kira na zamani. Ya kamata Malaman cikinmu da Daliban ilimi su yi amfani da shi wajen ilmantarwa da koyar da sahihin addini ga mutane, wani abu ne da ko da a yanzu ba a damu da kula rubuce-rubucen ilimin ba, nan gaba za a bukata kuma a amfana. Sai ya zama mutum ya bar kyakkyawar baya.


Haka kuma masana fannoni daban-daban na rayuwa, akwai bukatar su sadaukar da lokacinsu wajen bayyana nazarce-nazarce a kan fannonin da suke da sani a kai; fannin kiwon lafiya ne, tarihi ne, nazarin rayuwa ne, siyasa ne, ilimin halayyar dan Adam ne, da duk wani abu da sanar da wani shi zai zama mai amfani a gare shi, Allah kadai ne ya san ladan da zai ba wanda ya amfanar da mutane wajen kara inganta rayuwarsu.


Mu taimaka wajen yada ilmummukan wasu Malamanmu masu amfanarwa da zantukan bayin Allah da Hadisan Ma'asumai (AS) ingantattu, da nazarorin ma'abota hikima da fikiran addini. Sannan mu isar da nishadi da raha a junanmu da abin da bai wuce ƙima ba.


Ya kamata kowannenmu ya mayar da shafinsa ya zama kamar Mumbarin alkairi, irin muhallin da ko bayan ransa za a rika daukan bayanan da ya yi ko ya sharing ana yadawa da jindadi da farin ciki saboda tsaftarsu. Kar mu bari shafukanmu su zama gidan husuma da jayayya da cin mutunci da zage-zage, a cikin hakan akwai babban asara. Muna iya karfafa juna da yi wa junanmu nasiha a kan tsayuwa kyam da gwagwarmaya ba tare da mun soki kowa ko mun aibata shi ba. 


Ya Allah Ka sani mu gajiyayyun bayinKa ne, Allah Kai mana afuwa, Ka yafe gazawarmu, Ka cika mana da alkairi. Ya sa mu zama cikin mabiyanKa, kuma mataimakan BawanKa nagari (H), albarkacin Annabi Muhammadu dan Abdullahi da Iyalan Gidansa Tsarkaka (AS).


— Saifullahi M Kabir

18/01/2023 (25/6/1444).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post