Yadda yan Sandar Jihar Kano Suka Keta Alfarmar Matar Aure Ƴar Jarida Nazaiha Ibrahim.....

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Ƴan sanda a jihar kano sunci mutuncin yar Jarida, inda suka doketa har sai da aka kaita Asibiti, A halin yanzu tana kwance Rai a Hannun Allah. 


Yadda wasu yan sanda sukaci zarafin ma'aikaciyar Rahama Radio a wajen ɗauko rahoton rikicin yan KAROTA da sojoji Ranar juma'a da ta gabata, cin mutuncin 'Yan Jaridu a jihar Kano Abin takaici ne da Allah wadai.


Lamarin kullum kara girmama yake, ba tare da ita Hukumar yan sanda jihar kano tana daukan mataki akan masu cin mutuncin Yan Jaridu ba, 


ya kamata 

ukumomin da abin ya shafa su dau matakin da ya kamata dan kawo karshen cin mutuncin yan Jaridu, ba wannan shine karon farko ba, a watan daya gabata an ci mutuncin wani Dan Jarida a bakin aiki a jihar kano, inda Yan sanda su Duke shi, 


Muna kira ga IGP Usman Alkali Baba daya bada dama a bincike wannan lamari na cin mutuncin yan Jaridu da akeyi a bakin aiki, 


Tare da tabbatar da adalci wa Naziha Ma'aikaciya a gidan Radio na Rahama Radio dake kano.


Babban abin haushi Naziha ta kasan ce matar Aure ce,


Sakataren ƙungiya: Malam Umar El-faruk tare dasa Hannun Shugaban kungiyar Malam Barrah Almadany,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post