A ranar Juma'a 14/Jimada Sani/1444 H. Wanda yayi dai-dai da 07/01/2023m, Almajiran Malam Ibrahim Yaƙub Al'zakzaky (H) na Zon ɗin Fatima Zahara (S.A) suka gudanar da Mauludin Sayyida Zahra (S.a).
Bayan bude Taro da Addu'a da karatun Al'ƙur'ani mai girma an gabatar da ziyarar Sayyida Zahara (S.A). Sannan ƴan Ittihadu Shu'ara suka ƙara haska wajen da baitocin yabon Sayyida Zahra (S.A).
Babban baƙo mai jawabi a muhalin taron Mauludin Sayyida Zahra (S.a) shine, Malam Usman Sabo ATC.