Yau Alhamis Karim Younis dan kasar Palestine ya shaki iskan ‘yanci bayan shafe shekaru 40 yana tsare hannun jami’an tsaron haramtacciyar Isra’ila.
Karim ya sami kyakkyawar tariya daga yan uwa da Abokai na kasar Palestine. Karim yayi tambaya da ina mahaifiyarshi, ya nemi a kaishi kabarinta ya ziryaceta.
Mahaifiyar Karim ta rasu ne a watan Mayu na shekarar 2022, ta rasu sakamkon fama da tayi da jinyar hawan jini daya kamata sakamakon hanat ganin danta da jami’an tsaron HKI dake tsare da danta sukayi.
Yau Karim Younis ya shaki iskan yanci, kuma ya ziyarci makwancin mahaifiyar shi yayi mata addu’a cikin kuka da har sai da Abokai da masu rakiyarsa suka shiga tausayinsa da zubar da kwalla, Allah ya mata rahama ya kawo karshen wannan zalunci.
Labari: Al'ummar Palestines Ayau