@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Wani Malami ne ya tambayi ɗalibin sa; tsawon shekaru nawa kake almajirta a wuri na? Sai ɗalibin yace; tsawon shekaru 33. Sai Malamin yace; me ka koya daga gare ni tsawon waɗan nan shekaru? Sai ɗalibin yace; abubuwa 8 kawai na koya. Sai Malamin yayi mamaki tare da cewa; duk zaman mu da kai abubuwa 8 kawai ka koya daga gare ni. Ɗalibi yace; su kawai na koya kuma bana son yi maka karya.
Sai Malam yace; to fade su in jisu. Ɗalibi yace gasu kamar haka;
Na farko: nayi dubi zuwa ga mutane, sai naga kowanne mutum yana da aboki. Amma da zarar an kai shi kabari sai abokin ya rabu da shi. Sai na riki kyawawan ayyuka don mu shiga kabari tare da su.
Na biyu: nayi nazarin faɗin Allah Maɗaukaki "amma duk wanda ya ji tsoron tsayuwa gaban Ubangijin sa kuma ya hana zuciya son ranta, to Aljanna ce makomarsa". Sai nayi kokarin hana zuciya ta abinda take so don na dawwama akan yiwa Allah biyayya.
Na uku: nayi dubi ga mutane sai naga kowanne mutum yana da wani abu da yake da kima a wajen sa yana tattalinsa don kar ya rasa shi. Sai na tuna faɗin Allah Maɗaukaki "duk abinda yake wurin ku zai ƙare. Abinda ke wurin Allah shine zai dawwama". Sai ya zamana duk abinda ya fado hannu na zan mika shi ga Allah don ya kiyaye min shi kuma ya dawwama.
Na huɗu: nayi dubi ga mutane sai naga kowanne mutum yana alfahari da dukiyarsa ko matsayin sa ko nasabar sa. Sai na tuna faɗin Allah Maɗaukaki "Mafi daukaka a wurin Allah shine mafi Taqawa. Sai nake aikin Taqawa don na zamto mai girma a wurin Allah.
Na biyar: nayi dubi ga mutane sai naga suna yiwa junansu hassada akan ni'imomin duniya. Sai na tuna faɗin Allah Maɗaukaki "mune muka raba muku abubuwan rayuwar duniya". Sai na fahimci cewa Allah ne yayi rabon don haka na bar hassada.
Na shida: nayi dubi ga mutane sai naga suna adawa da junansu. Har suna kisan juna. Sai na tuna faɗin Allah Maɗaukaki "Hakika Shaidan makiyi ne a gareku, ku rike shi makiyi". Sai na bar adawa da mutane na koma adawa da Shaidan kawai.
Na Bakwai: nayi dubi ga mutane sai naga kowanne mutum yana wofantar da kansa tareda wulakantar da kansa wajen neman arziki. Sai na tuna faɗin Allah Maɗaukaki "babu wata dabba a bayan kasa face arzikin ta yana kan Allah". Sai na fahimci ai nima ɗaya ne daga cikin dabbobin. Sai na himmatu da abinda Allah yake dashi a kaina, ba abinda nake dashi a kansa ba.
Na Takwas: nayi dubi ga mutane sai naga kowanne mutum yana dogaro ga mutum ɗan uwansa. Ko don saboda kuɗin sa ko matsayin sa. Sai na tuna faɗin Allah Maɗaukaki "Duk wanda ya dogara ga Allah, ya isar masa". Sai na bar dogaro ga mutane, na dogara ga Allah Mahalicci.
Sai Malamin yace; daga yau kai ne Malamin, ni na koma ɗalibin ka.