Dalilin Haka Zakaga Mutum Yana Rayuwa a Cikin Abubuwa Guda Biyu, Tsakanin Tsoro Da Saka Tsammani,Yana Tsoron Kowane Lokaci Mutuwa Zata Iya Riskarshi,Kuma a Lokaci Daya Yana Tunanin Kila Ya Jima Yana Morar Rayuwar Tasa.
Kullum Dan Adam Mai Iltizami Da Dokokin Allah Yana Rayuwa Ne Mai Yin Addua Allah Yasa Yayi Kyakkyawan Karshe,Kuma Ya Tsiratar Dashi Daga Wutar Jahannama.
Dayawan Mutane Bayan Sun Mutu Zasuyi Kwadayin Allah Ya Dawo Dasu a Cikin Wannan Duniya,Kuma Su Dauki Alkawarin Zasuyi Aikin Alkhairi Sabanin Wanda Sukayi a Rayuwarsu a Baya,Nan Take Jawabi Zaizo Daga Mahalicci Cewa Babu Wannan Damar,Duk Wata Dama Da Zaa Baku An Baku,Wasunku Sunyi Rayuwa Fiye Da Shekaru Hamsin a Duniya Amma Sun Kun Kasa Yin Aikin Kirki Dan Haka Wannan Damar Bakuda Ita a Yanzu.
Da Wannan Zamu Fahimci Cewa Wannan Damar Da Allah Taala Ya Bamu a Cikin Wannan Duniya Da Muke Rayuwa a Yanzu,Babba ce Daga Cikin Manya Manyan Niimomin Da Allah Taala Yayi Mana Domin Ingantar Rayuwar Mu Ta Har, abada,Maana Yanzu Mukeda Damar Dazamuyi Aikin Alkhairi Domin Riskarsa a Gobe.
Wajibi Ne a Garemu Mu Godewa Allah Taala Akan Wannan Niima,a Baki Da Zuciya Da Kuma Aiki Na Gabobi,Da Kuma Amfanuwa da Wannan Damar Ta Shekarun Da Allah Yayi Mana Niima Dasu a Yanzu Wajen Dabbaka Hadafin Halittar Mu a Cikin Wannan Duniya Wato (Ibada).