Wanda ya yarda An yiwa Annabi Sihiri Yayi Ridda Sai Yanka......!!!




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Cewar Sheikh Malam Alhaji Abubakar Mahmoud Gumi, Allah ya masa rahama!


Malamin ya fadi haka a lokacin tafsirin Alkur'ani da ya ke yi a lokacin da aka ja masa wannan ayar:


Bismillahi -----------------


وَبِٱلْحَقِّ أَنزَلْنَٰهُ وَبِٱلْحَقِّ نَزَلَ ۗ وَمَآ أَرْسَلْنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرًا وَنَذِيرًا


A cikin sharhin da ya yi har yake cewa Allah Ya yi alkawali zai kare Alkur'ani amma bai yi irin wannan alkawalin na kariya ga Bukhari ko Muslim ba. A daidai nan almajirai suka taso da tambayoyi, shi kuma yana cewa su fadada bincike, har yake cewa wanda ya yarda an yi wa Annabi sihiri ya yi ridda sai yanka. Hayaniyar almajirai masu tambaya ta yawaita, sai ya kare kansa da cewa: kun taba ji na ce an yi wa Annabi sihiri? Babu amsa!


SHARHI


Kamar malam yana cewa akwai hadissai a cikin littafin hadisi na Bukhari da ke tabbatar da cewa wai an yi wa Annabi sihiri, kuma yarda da hakan ridda ne kuma zagi ne ga Annabi wanda hukumcinsa shi ne kisa!! Kuma kamar malam yana cewa wadannan hadissan karya ne aka cusa cikin ingantattun littattafan musulumci. Ma'anar wannan shi ne warware da'awar da ake yi kan cewa littafin hadissai na Bukhari sahihi ne, shi yasa almajiransa su kai ta hayaniya domin sun ji malam ya musa wata hakika da aka dora su akai da dadewa.


Almajiran Malam fa sun hango hatsarin da ke tattare da furucin malam, sun hango cewa muddin maganar malam ta zama gaskiya to:


1. Muhammad Bin Isma'il Albukhriy ya yi ridda, domin ya ce an yi sihirin.


2. Mazajen hadisin masu cewa haddasana an wane duk sun yi ridda.


3. Rawin a'ala na hadissan wato Sayyida A'isha da wasu sahabban wadanda suka ce an yi sihirin wai kuma har sihirin ya yi tasiri ga Annabi wai har Annabi (Sawa) yana aikata abu bai san ya aikata ba, to duk cikarsu sun yi ridda.


4. Almajiran malamin sun rude sabo da muddin aka ce kunzumin maruwaitan nan da taron sahabban can aka ce sun yi ridda to kuwa fa akwai matsala! Matsalar ita ce mu musulmi kenan mun samo addininmu daga wadanda suka yi ridda wa addinin tun dauri? Kenan jabun addini ba na Annabi (S) muke yi ba, wato son ran wasu ne muka rika a matsayin addini???


Kun ga ai dole almajirai su rude!!!!


Amma mu ba za mu rude ba, domin tun asali kuskure ne cewa dukkan hadissan da ke cikin wani littafi wanda mutum ya rubuta daga kokarinsa wai mu yarda komai sahihi ne bisa yakini!! 


MU KALLI MATANIN HADISI DAYA KACAL, DOMIN KU GOYI BAYAN MALAM GUMI AKAN CEWA WANNAN HADISIN KARYA NE AKA CUSA CIKIN ADDININ MUSULUMCI!!


5763- حَدَّثَنَا إِبْرَاهِيمُ بْنُ مُوسَى، أَخْبَرَنَا عِيسَى بْنُ يُونُسَ، عَنْ هِشَامٍ، عَنْ أَبِيهِ، عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: سَحَرَ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ رَجُلٌ مِنْ بَنِي زُرَيْقٍ يُقَالُ لَهُ: لَبِيدُ بْنُ الأَعْصَمِ، حَتَّى كَانَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ يُخَيَّلُ إِلَيْهِ أَنَّهُ كَانَ يَفْعَلُ الشَّيْءَ وَمَا فَعَلَهُ، حَتَّى إِذَا كَانَ ذَاتَ يَوْمٍ أَوْ ذَاتَ لَيْلَةٍ وَهُوَ عِنْدِي، لَكِنَّهُ دَعَا وَدَعَا، ثُمَّ قَالَ: يَا عَائِشَةُ، أُشْعِرْتُ أَنَّ اللَّهَ أَفْتَانِي فِيمَا اسْتَفْتَيْتُهُ فِيهِ؛ أَتَانِي رَجُلانِ، فَقَعَدَ أَحَدُهُمَا عِنْدَ رَأْسِي، وَالآخَرُ عِنْدَ رِجْلَيَّ، فَقَالَ أَحَدُهُمَا لِصَاحِبِهِ: مَا وَجَعُ الرَّجُلِ؟ فَقَالَ: مَطْبُوبٌ، قَالَ: مَنْ طَبَّهُ؟ قَالَ: لَبِيدُ بْنُ الأَعْصَمِ، قَالَ: فِي أَيِّ شَيْءٍ؟ قَالَ: فِي مُشْطٍ وَمُشَاطَةٍ وَجُفِّ طَلْعِ نَخْلَةٍ ذَكَرٍ، قَالَ: وَأَيْنَ هُوَ؟ قَالَ: فِي بِئْرِ ذَرْوَانَ، فَأَتَاهَا رَسُولُ اللَّهِ ﷺ فِي نَاسٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَجَاءَ فَقَالَ: يَا عَائِشَةُ، كَأَنَّ مَاءَهَا نُقَاعَةُ الحِنَّاءِ، أَوْ كَأَنَّ رُؤوسَ نَخْلِهَا رُؤوسُ الشَّيَاطِينِ، قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَفَلا اسْتَخْرَجْتَهُ؟ قَالَ: قَدْ عَافَانِي اللَّهُ، فَكَرِهْتُ أَنْ أُثَوِّرَ عَلَى النَّاسِ فِيهِ شَرًّا، فَأَمَرَ بِهَا فَدُفِنَتْ


Astagfirullah! Astagfirullah!! Astagfirullah!!!


Ni kam na yarda cewa labarin nan na sama karya ne aka tsara domin a saka shakku cikin annabtar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi! Hukumcinsu na ga Allah mahaliccinsu!! Amma mu ba za mu bi su bisa wannan kuskuren ba!!!


Abu na biyu, akwai malaman da suka takarkare wajen sharhantar hadisin da yi masa tawili, wai sihiri iri biyu ne da na kaza da na kaza! Ko kuma masu cewa wai ai duk da kasancewar sihirin ya yi tasiri wa Annabi to bai shafi wahayi ba!! Ajii!!! Ta wace hanya, oho, babu bayani sai da'awa ta fatar baki kawai!!!


Idan kun lura dukansu suna wanke maruwaitan da mai littafin, amma sun bar Annabi cikin matsala, sun bar addininmu cikin matsala. Suna son bisa tilasci sai sun tabbatar da ismar littafin Bukhari ta dabara, ba tare da sun kula cewa kuma ta wani gefen kuma sun zagi Annabi (S) ba!! Wannan gafala ce, mu kuma ba za mu bi su bisa irin wannan gafalar ba. Za mu ce:


WANNAN HADISIN KARYA NE KO DA WANI ZAI TOZARTA, DOMIN ANNABI AKA AIKO MANA, KOWA WADA NE ANNABI NE KAWAI MAI KYAKKYAWAN DIRI DA TSAYI. SAM-SAM BA ZA MU LAMUNCI A WANKE WANI A SHAFAWA ANNABI DATTI BA!! 


DOMIN KO WAYE ANNABI YA FI SHI!!!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post