@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
Yau 13 ga watan Jumada Sani , wanda yayi dai-dai da ranar wafatin Sayyida Ummul Baneen (Faɗimatu bintu Hizam ) matar Imam Ali (a.s.) , mahaifiyar jarumi , kwamandan Imam Hussein Abul Fadlil Abbas da yayi shahada tare da ƴan uwansa uku a filin karbala , tayi wafati a irin wannan rana mai kamar ta yau a shekara ta 64 daga hijirar Annabi (s).
Babu shakka Sayyida Ummul Baneen Samfuri ce , abar kwaikwayo wajen Wilaya da sallamawa Ahlul Baiti , Ƙaunarsu da nuna damuwa da alhini cikin musibun da suka samesu bayan Annabi (s) .
Ta kasance idan tana kuka da karanta ƙasidunta na juyayi ga Imam Hussain har zuƙatan maƙiya Ahlul Baiti sukan yi taushi dan jinsu .
lokacin da Bishir yazo da labarin kashe Imam Hussain (a.s.) ga mutanen Madina tazo tana kuka tana faɗin ina masoyina ɗa na Hussaini ? Bishir yace mata ina miki ta'aziyya da rasa ɗanki Abbas ! Ta ce masa ba wannan nakeson ji ba , ina masoyina Al-Hussain ? Ya sake ce mata ina yi miki ta'aziyyar shahadar ɗan ki Ja'afar , ta sake ce masa ba wannan nake son ji ba , ina masoyina Al-Hussain ? Bishir yace ina yi miki ta'aziyya da baƙin cikin sanar dake kashe ɗan ki Abdullahi ! tace masa Ni fa ba wannan nake son ji ba ina labarin ɗana Al-Hussain ? Yace mata an kashe miki ɗanki Usman a karbala ! Ta sake ce masa ina labarin Masoyina Al-Hussain yYau 13 ga watan Jumada Sani , wanda yayi dai-dai da ranar wafatin Sayyida Ummul Baneen (Faɗimatu bintu Hizam ) matar Imam Ali (a.s.) , mahaifiyar jarumi , kwamandan Imam Hussein Abul Fadlil Abbas da yayi shahada tare da ƴan uwansa uku a filin karbala , tayi wafati a irin wannan rana mai kamar ta yau a shekara ta 64 daga hijirar Annabi (s).
Babu shakka Sayyida Ummul Baneen Samfuri ce , abar kwaikwayo wajen Wilaya da sallamawa Ahlul Baiti , Ƙaunarsu da nuna damuwa da alhini cikin musibun da suka samesu bayan Annabi (s) , idan tana kuka da karanta ƙasidun ta na juyayi ga Imam Hussain har zuƙatan maƙiya Ahlul Baiti sukan yi taushi dan jinsu , lokacin da bishir yazo da labarin kashe Imam Hussain ga mutanen Madina tazo tana kuka tana faɗin ina masoyina , ɗa na Hussaini ? Bishir yace mata ina miki ta'aziyya da rasa ɗanki Abbas ! Ta ce masa ba wannan nakeson ji ba , ina masoyina Al-hussain ? Ya sake ce mata inai miki ta'aziyyar shahadar ɗan ki Ja'afar , ta sake ce masa ba wannan nake son ji ba , ina masoyina Al-hussain ? Bishir yace inai miki ta'aziyya da baƙin cikin sanar dake kashe ɗan ki Abdullahi ! tace masa Ni fa ba wannan nake son ji ba ina labarin ɗa na Al-hussein ? Yace mata an kashe miki ɗanki Usman a karbala ! Ta sake ce masa ina labarin Masoyina Al-Hussain ? yace mata an kashe Al-Hussain a filin karbala , take ta fashe da kuka tare da duk wanda ke wurin .
Ya zo a ruwaya daga Imam Sadik (a.s.) cewa : Sayyida Ummul Banin ta rasa idonta (ganinta) saboda kukan da take na juyayin abunda ya sami Imam Hussain (a.s.) .
السلام عليك يا شريكة زينب في المصائب
😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey