TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR SHAHEED HAMEED ZAKZAKY (H) A ABUJA.




kamar yadda yake a jadawali, ranar Talata 17/1/2023, ita ce rana ta biyu kuma ta 'karshe a cikin jerin kwanakin da aka dauka ana gudanar da bukukuwan tunawa da zagayowar ranar da aka haifi Shaheed Hameed Zakzaky (H) a garin Abuja.


Da safiyar ranar an gudanar da Saukar karatun Qur'ani mai girma, sannan aka gabatar da addu'o'i zuwa ga ruhin Shaheed Hameed da sauran Shuhada.


Bayan haka, da yamma  an gudanar da zikira ta tunawa Shuhada da suka ba da rayukansu a tafarkin Allah. 


Da dare kuma a nan ne aka gudanar da 'kayataccen bikin na musamman akan wannan Gwarzon Shaheedin, wato Hameed Zakzaky, Inda aka gabar da abubuwa daban-daban. 


Bayan bude taro da addu'a, Wa'ko'kin yabo, sai aka yi paper Presentation; sanna aka saurarai Jawabi daga bakin Umma Zeenatuddeen Ibraheem Zakzaky. A lokacin gudanar da taron, an kaddamar da butun-butumin hannu mai motsi da aka 'kir'kira na Shaheed Hameed, tare da display na girmamawa. 


Daga karshe an raba kyaututuka; aka yanka cake sai aka yi addu'a aka sallami Jama'a


18/1/2023,

Fa'eez Media.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post