Tuna baya: Farkon Fara Muzaharar Neman A Saki Sheikh Zakzaky Ta Kullum a Abuja....!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



A ranar 8 ga watan Janairun 2018 ne yan uwa almjiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) su ka fara jerin gwano a kowace rana, a babban birnin tarayya, Abuja. 


Muzaharar ta kira ga gwamnatin tarayya ce kan ta saki Sheikh Ibraheem Zakzaky da maidakinsa, wanda su ka tsare a 14 ga Disambar 2015 bayan kisan kiyashin Buhari a Zariya.


Jerin gwanon wanda yake na lumana ne, ya fara a babbar Sakateriya ta kasa, sai dai kafin karewa jami'an tsaron ya sanda sun bayyana inda su ka farmki masu jerin gwanon da harbi. 


Mutane da yawa su ka samu rauni sakamakon harbin bindigar, yayin da su ka kama adadi mai yawa. Sun yi harbi mummuna kan masu jerin gwanon lumana marasa dauke da makami, wanda laifin su shi ne sun yi kira ga gwamnati da ta bi umurnin kotu.


Tun bayan fara Muzaharar a wannan ranar, an ci gaba da fitowa kowace rana a Abuja ba tare da fasawa ba har sai da gwamnati ta saki malamin da maidakinsa, a 28 ga watan Yulin 2021, kusan shekara 4 da ci gaba da jerin gwanon kenan. 


A tsawon shekarun, gwamnati ta farmaki masu jerin gwanon a lokuta daban daban, inda ta kashe mutane da dama tare da raunata daru-ruwa da kuma kamawa.


Dai daga cikin harin, shi ne na Oktobar 2018 yayin Tattakin Arbaeen na Imam Hussain a Abuja, inda su ka kashe akalla mutum 40. A harin, wanda rundunar fadar shugaban kasa da gamayyar yan sanda su ka kai, sun kashe mata, yara da yan makaranta, ciki har da mai hidimar kasa (NYSC). 


Haka ma a babbar sakateriya ta kasa, 22 ga Yulin 2019, sun kashe adadi tare da kama wasu yayin jerin gwanon kira ga gwamnatin, inda su ka kai su ofishin SARS a Abuja, takai ga wani ya rasa ransa sakamakon raunukan harbin bindiga da rashin kulawar likitoci, har yanzu su na ci gaba da tsare su a gidan yari bayan kwashe wasu marasa lafiya a asibiti a wani aikin rashin imani na jami'an. 


Ya zama wajibi gwamnati ta saki dukkan yan uwan da take tsare da su a wuraren tsarewa da gaggawa. 


- Kwamared Abdulmemeen Salisu 

The Youngest Activist

8 ga watan Janairu, 2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post