TARON TUNAWA DA SHAHADAR QASEEM SULEIMANI DA ABU MAHDI AL-MUHANDIS A GARIN KANO

 



Yan uwa na Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Zakzaky, (H) a Kano, sun gabatar da taron tunawa da gwarazan Shahidai na duniya wato Qaseem Suleimani da Abu Mahdi Al-Muhandis karo na uku.


Bayan bude taro da addu'a, sai karatun Qur'ani mai girma daga bakin alarammomi na Harkar Musulunci, sai mawaka su ka rero wake na jinjina ga gwarazan shahidan.

Malama Imamu Ya'aqub Kurna ne ya gabatar da malamai ma su jawabi.


Malama Nura Jogana shi ne mai jawabi na farko, bayan ya kammala sai malami na biyu, Sheikh Sayyid Kidir ya yi nashi jawabin, sai jawabin bako na musamman, Malam Ibrahim Aqeel, a cikin jawabin nasa, ya kawo irin sadaukarwa, sallamawa da kuma kokari na waddannan bayin Allah a kan jajircewa don taimakon raunana a fadin duniyar muslunci.


Bayan nan, sai Intizarul Imam Mahdi (ATFS) su ka gabatar da faretin girmamawa na Salam Farmande tare da girmamawa ga Shahidai da kyautukan furen fulawa, inda manyan baki suka mika nasu sai iyaye sistoci, sai kuma Fulani daga karshe.


Bayan nan sai aka saurari jawabin jagora wanda ya yi akan tunawa da irin wannan rana ta Shahidan cikin harshen turanci karo na uku (03/01/2023).


Daga karshe, wakilin 'yan uwa na Kano, Dr. Sunusi Abdulkadir Koki ya yi jawabin rufewa kan Shahidan da kuma Shahid Nimr, inda ya tabo bangaren  rayuwarsu da darussan tsayuwarsu na fada da zalunci. Sai a ka yi addu'a a ka tashi. 


Taron wanda shi ne karo na uku, an gudanar da shi ne a Masallacin Fage da ke Kano, dimbin mahalarta ne su ka samu halartar taron. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post