Tarihin Kasuwar Wafa Da ke Fagge Kano !!!

 




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Shimfida 


Kasuwar Wafa, kasuwar ƙasa-da-ƙasa ce a cikin garin Kano wacce  ake gudanar da hada-hadar saye tare kuma da sayar da kuɗi zalla a cikinta. Wato kasuwa ce ta hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen duniya. Babu wata ƙasa a duniya da ake irin wannan hada-hada wacce ba ta da dangataka da wannan kasuwa ta Wafa mai matsugunni a Unguwar Fagge a cikin birnin Kano a Najeriya.


Tarihi 


Ana kyautata zaton cewa, wannan kasuwa ta Wafa ta samo asali ne tun kafin samun ‘yancin kan Najeriya, zamanin da Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya gina Tsohuwar Tashar Kuka, wacce ta sabauta samuwar wannan kasuwa mai ci har yau ɗin nan take cigaba da wanzuwa. Shi kuwa marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya yi wa’adin mulkinsa ne daga shekarar 1953 zuwa 1963.


Amma zaman daram kuma ya faro ne daga farkon hawa mulkin Marigayi tsohon Gwamnan farar hula na farko a Kano Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi wanda ya gina gidan jaridar Tirayomf a guribin tashar a cikin shekarar 1983 ko 1984.


Tun asali, wannan tasha, tasha ce wadda ke safarar mutanen ƙasashen waje musamman Yankin Yammaci kamar irin su garuruwan Agadas wacce a yanzu take cikin jamhuriyar Nijar; mutanen Libiya; mutanen Algeria; Mali da sauransu. Da kuma Yankuna Gabas mai nisa kamar irin su Chadi, Kamaru, Sudan da kuma sauran sassan duniya waɗanda hada-hadar wata cinikayya take kawo su Kano ko dai domin su saya ko kuma domin su sayar.


Irin waɗannan baƙi da suke shigowa daga ƙasashen waje, sun kasance suna da masauki a gefen tashar a wani yanki na Unguwar ta Fagge. Wannan masauƙi kuwa hotel ne mallakin wani mai kuɗi Alhaji Mamuda Alhassan Ɗantata kuma sunan hotel ɗin Wafa, wanda shi kansa Mamudan ya shahara da sunan hotel ɗin wato Mamuda Wafa.


Bayan haka kuma, sunan wannan hotel ɗin shi ne dai ya sake zama sunan wannan fitacciyar kasuwar hada-hadar kuɗaɗe a duniya; wato Wafa. Sannan kuma akwai ƙananan gidaje da ake amfani da su a kewayen wajen a wancan lokacin wajen gudanar da wannan sana’a ta saukar baƙi.


Sannu a hankali waɗannan rukunin gidaje aka riƙa gudanar da harkar canjin cajin kuɗi a cikinsu tare kuma da saukar baƙi a cikin wasu. Amma da tafiya-ta-yi-tafiya, sai aka daina saukar kowa aka mayar da gurin ko na ce unguwar gurin canjin kuɗi zalla kamar yadda yake a yau.


Akwai wasu mashahuran mutane waɗanda sunayensu suka yi fice wajen saukar waɗannan baƙi a wancan lokacin. Daga cikin su akwai Sulen Dela, wanda yake kula da baƙin da suke fitowa daga yanki Gabas da suka haɗa da  Mutanen Chadi, Kamaru da kuma mutanen garuruwan Barebari daga nan cikin gida Najeriya.


Sai kuma Alhaji Muhammadu da Alhaji Wada Kura da suke kula da mutanen da suke fitowa daga Arewa mai nisa kamar irin su Nijar, Mali, Libiya, Algeria da sauransu.


Akwai kuma Alhaji Abdulhamidu da yake kula da mutanen da suke fitowa daga yankuna Arewa ta kusa kamar irin su Maraɗi, Yamai, da sauransu.


Sai kuma Alhaji Sani Ɗan-canji wanda aka fi sani da Alhaji Sani Cuku-Cuku yake kula da baƙin cikin gida Najeriya.


Duk baƙin da suka zo da kuɗaɗen ƙasarsu, waɗannan jama’a da sauran abokan aikinsu su suke jagorantar musayar kuɗaɗen na su zuwa na gida Najeriya domin su shiga kasuwannin da suke buƙata su sayi hajar da ta kawo su.


Haja


Babu wata haja da ake sayarwa a wannan kasuwa da ta wuce kuɗi. Kasuwar kuɗi ce zalla.


Sai dai, suna gudanar da hulɗoɗin da suka shafi kuɗi kamar tura kuɗi da kuma karɓar kuɗi daga kowace ƙasa ta duniya kuma kowane irin kuɗi ne matuƙar dai ana buga shi a takarda. E, mana, kasan ai akwai kuɗin da ba buga shi ake yi a zahirance ba kamar Bitcoins. Kodayake a iya binciken da na gudanar ban tuntuɓe su game da wannan ba. Saboda haka tana iya yiwuwa suna hada-hadar Bitcoins ɗin ma.


Abokan Hulɗa


Kusan babu wata ƙasa a duniya wacce bata hulɗa da wannan kasuwa ta fuskacin canjin kuɗaɗe.


Magarar Wannan Rubutun


Tattaunawa da Alhaji Yusuf Nabahani Daraktan Kamfanin Mailima BDC, Fagge, Kano a ranar 2/1/2019.


Tattaunawa ta Wayar Tarho da Alhaji Musa Gwadabe. Kwamishina a Zamanin Gwamnatin Audu Baqo. A ranar 4/1/2019.


Ziyarar Gani-da-Ido. A ranakun 27/12/2018 da kuma 1/1/2019.


Rumbun Ilmi ✍️

Saliadeen Sicey ✍️


31/1/2023.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post