[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Hameed Week.
®Hamidiyyun Press.
An haifi Sayyid Hamid a ranar 17 ga watan Janairu 1992 wanda yai dai-
dai da 13 ga Watan Rajab 1412. Hijiriyya. a unguwar Gwarbai cikin birnin Zaria dake jihar kadunan tarayyar Nijeriya.
Sayyid Hamid ya taso a gidan girma gidan Ilimi da Mutunci gidan da ya
hada komai na rayuwa a duniya da lahira, gidan da ya kai makura a
sanin Addini da rayuwar zamani.
Sayyid Hamid ya fara karatun sa ne a gurin iyayen sa wadanda suka gina
masa ginshiqin karatuttukan sa na ibada dana sana'a wadanda mu a
wurinmu dukkan su Ilimomin Addini ne.
Ba sai na bada labarin hazakar Sayyid Hamid ba, domin ga masu
bibiyar zantukan Allamah Zakzaky sun sha jin irin baiwar da Allah (T)
ya kimsa a kwakwalwar Sayyid Hamid marhum, ya zama wani irin Zaki
a fagen masu hazaƙa banji ko ganin wani dalibi da Sayyid Hamid yai
gogayya dashi a fagen ilimi bai sallama masa ba! Sayyid Hamid yayi karatun Nursery da primary dinsa ne a makaranta BUKS International dake daura da Aviation dake sabon garin Zariya.
Daganan ya koma makarantar Tabo School inda yai karatun Secondary
Junior ya sake komawa makarantar Hallmark International inda ya fara
Senior Secondary aji ɗaya daganan saiya sake komawa makarantar
Zariya Academy inda ya kammala karatunsa na SSCE.
Sayyid Hamid ya kasance yana yawan ƙorafin su makarantun basa karatu yanda ya kamata kuma hakan ya sashi yawan canza guraren
karatu daganan zuwa can, a duk lokacin da suka kaiwa Malam (H) korafin cewa makaranta basa karatun da yadace sai Sayyid (H) yasa a bincika idan ta tabbata haka ne sai a bincika inda ake ganin ya dara nan, kuma haka za'ayi matuƙar yaran Malam (H) suna san makaranta sabo da kyawun tsarin karatun tasu ba makawa matuƙar zasuyi karatun can za'a nema masu.
Sayyid Hamid ya maida hankalinsa sosai wajen bincike bincike a kan
nau'in karatuttuka daban-daban tun kafin ya sami shiga Jami'a a birnin
Beijing dake China.
Hamidiyyun Press✍
16 January, 2023