Takaitaccen Tarihin Sayyada Fatima (A's)....!!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 

 

Sayyida Fatima al-Zahra (As) – Matar Aure:  

 

 

Fatima ta tare a dan karamin gidan mijinta Ali bin Abi Dalib (As.) alhali tana mai farin ciki da amincewa da shi. Ta rayu tare da mijinta cikin kwanciyar hankali da farin ciki, ko da yaushe tana cikin sakin fuska, tsananin rayuwa ma taba raba gidanta da farin cikinsa ba. Ita ce matar Ali gwarzon Musulunci, ma’abucin sadaukar da kai kuma mai dauke da tutar jihadi da nasara. 

 

Fatima (As) ta kasance ita ma daidai da haka. Ta kasance tare da Ali kamar yadda mahaifiyarta Khadija ta kasance tare da Manzo (S), tana gamayya da shi ciki jihadinsa, tana kuma hakurewa wahalhalun rayuwa, don haka sai ta aiwatar da aikinta daidai da yadda Allah Madaukaki Ya zabe ta don shi. 

 

Ali da Fatima (As) sun rayu a inuwar Manzo (S) kuma karkashin kulawarsa. 

Manzo ya ba Fatima abin da bai ba kowa ba bayan aurenta, ta yadda tsananin lurarsa da ta’allakar zuciyarsa da ita har ya kai in zai yi tafiya ko zai je yaki Fatima ce karshen wadda ke sallama da shi. Kuma idan ya dawo daga tafiyarsa ko yakinsa Fatima ce farkon wadda ya ke fara haduwa da su daga mutane. 

 

Fatima (As) ta rayu a gidanta a matsayin uwar-gida; tana lura da al’amuran  gidanta kuma tana aiwatar da bukatun gidan bisa dogaro da kokarinta. Bata kasance tana da masu hidima ko bayi ko ‘yan aiki ba. Duk rayuwarta ta kasnce jihadi ne da kokari. 

 

Fatima ta kasance tana nika sha’iri, ta yi amfani da dutsen nika da hannunta, tana yin Alkubus da kanta, tana share gida kuma tana aiwatar lizimce-lizimcen iyali. 

 

Hakika kuma Manzo (S) da Ali (As) sun kasance suna ganin haka daga Fatima, kuma suna tarayya da ita a cikin wahalhalun, suna kaskanta wahalhalun rayuwa a idonta. Ali (As) ya kasance yana taimakonta a aikace- aikacen gida da gudanar da al’amuransa. 

 

An ruwaito cewa Manzo (S) ya taba shiga wajen Fatima, sai ya same ta tana kuka a lokacin tana nika alhali tana sanye da wani mayafi na fatar rakumi. Yayin da ya ganta sai ya yi kuka ya ce: “Ya Fatima, jure dacin rayuwar duniya a yau da ni’imar gobe lahira. Sai Fatima ta ce: “Ya Manzon Allah, godiya ta tabata ga Allah a kan ni’imominSa” 

 

Haka Manzon Allah (S) da Ahlulbaiti (As) ke ba mu darussan rayuwa da tsarkakken misali na shugabanci a Musulunci. Ina Musulunci da irin rayuwar holewa da jin dadi na fajirci da muke gani a yau? Ina tarihin yanayin rayuwar al-Mustafa (S) da tsarkakan iyalansa da irin girman kan mawadata da almubazzarancin masu hannu-da-shuni alhali a gab da su akwai dubban mayunwata da matalauta? 

 

________ 

1- Abul-Hasan Waramu bin Abi Firas al-Astari, al-Maliki, a cikin Tanbihul- Khawadiri wa Nuzhaul-Nawaziri, juzu’i na 2, shafi na 230. 

 

 

 

Mu hadu a kashi nagaba domin cigaba da karanta Tarihin "Sarauniyar Matan Duniya da kuma lahira  (Kiyama). 

 


     —Jawad Adamu Tsoho


 

#ZahraDay

#HappyMaulud

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post