[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Har yanzu duniya ta kasa daina mamakin me ya sa kamfanin Facebook ya zare zunzurutin kudi har $19 billion don sayan manhajar WhatsApp a lokacin da darajarta ba ta wuce $1.5 billion ba.
Wasu mutane guda biyu da ake kira Brian Acton da Jan Koum su suka kirkiri manhajar WhatsApp bayan sun bar aiki a kamfanin Yahoo. Hakan ya faru ne bayan Brian Acton ya nemi aiki a kamfanin Facebook amma bai samu ba.
Samar da manhajar WhatsApp shi ya canja tsarin yadda duniya take mu'amala da dandulan sada zumunta cikin sauki, wato ya kawo wasu sababbin tsarukan da suka yi matukar dacewa da zamani kasantuwar bayyanar wayar iPhone wacce kamfanin Apple ya kaddamar.
WhatsApp ya kawo tsarin mu'amala da mutane cikin sauki kuma cike da tsaro, ta yadda ko kamfanin ba zai iya ganin bayanan mutane wato abun da suke turawa a tsakaninsu ba.
Ganin yadda manhajar ta samu karbuwa a duniya cikin kankanin lokaci hakan ya janyo hankulan manyan kamfanonin duniya kamar su Google, Microsoft da sauransu don su saye ta, wasu kuma su zuba hannun jari.
A lokacin WhatsApp ya samu kudade sosai, inda aka hada darajarsa ta kai $1.5 billion bayan ya samu kudaden da aka zuba masa hannun jari.
Ganin yadda ya samu karbuwa a duniya ya sa hankalin Mark Zuckerberg ya juyo kansa, inda ya nemi wadannan mutanen suka zauna, kuma ya nemi ya sayi wannan manhajar. A lokaci daya ya taya ta $19 billion, wato makudan kudaden da ba za su iya cewa ba za su sayar ba.
Haka nan ya ce za su ci gaba da tafiyar da manhajar kuma su ci gashin kansu. Hakan ya sa suka amince suka sayar da ita, aka ba su cash da kuma stock. Hakan ya faru ne a shekarar 2013.
Har a lokacin WhatsApp ba ya samun komai, wato ba shi da source of income, saboda ba a saka ads a manhajar, kuma kyauta ce ba a biyan ko sisi don amfani da ita.
Sanin cewa yawancin kamfanonin yanar gizo a haka suke samun kudadensu, kuma ga shi wannan manhajar ba ta samun kudi a daya daga cikin wadannan, hakan ya sa hankalin mutane ya tashi a duniya suna so su ji shin ta yaya wannan manhajar take samun kudi, suna tsoron kada ya kasance bayanan mutane suke sayarwa.
To da farko dai mu san cewa Mark Zuckerberg ya fitar da wadannan makudan kudaden daga Facebook har $19 billion ya sayi WhatsApp ne saboda kada ya zama abokiyar hamayyarsu wato competitor, saboda WhatsApp ya fi Messenger yawan jama'a.
Ya yi tunanin cewa idan ya bar manhajar ta samu daukaka fiye da yadda ake tunani to tabbas zai zamar musu babbar barazana, don haka abun da ya fi alheri shi ne su saye ta.
To amma ya ji labari cewa Brian Acton da Jan Koum za su iya yin taurin kai wajen sayar da wannnan manhajar, saboda ta janyo hankulan kamfanoni da dama, don haka ya taya ta da zunzurutin kudaden nan ta yadda ba za su iya rejecting ba.
To yanzu mu dawo kan batunmu, ta yaya WhatsApp yake samun kudi?
Shekarun baya WhatsApp ya kawo tsarin biyan $1 wacce take matsayin donation a wasu kasashen ta hanyar amfani da WhatsApp Businesss kusan kamar yadda Wikipedia yake yi tunda shi ma ba ya amfani da ads kuma free ne.
Amma daga baya WhatsApp ya cire wannan tsarin, kuma har yanzu bai sanar da duniya inda yake samun kudi ba.
Tabbas hakan ya kara jefa kamfanin cikin zargi, ana tunanin anya ba bayanan mutane yake sayarwa ba? Haka nan dai hukumomi suna tuhumar kamfanin da wannan batun.
Bayan wannan wata badakalar ta sake faruwa a kamfanin inda makirkiranta suka bar aiki a kamfanin. Wannan ma ya sake janyo cecekuce a duniya
Daga shafin Mohiddeen Online: https://mohiddeen.online/post/970844-ta-yaya-whatsapp
—Muhammad Auwal Ahmad (#Mohiddeen)