Wannan ma'aikacin Banki mai suna Monday yana tilasta karban kudi a gurin 'yan uwan mu kafin ya canza musu kudi a garin Hadejia
Duk Naira dubu dari yana karban cin hancin Naira dubu daya, akwai wani abokina jiya ya kai Naira Miliyan daya a saka masa a account sai da Monday ya kwace masa Naira dubu 10
Watakila wasu sun fuskanci irin wannan zalunci da kwace a wasu Bankuna, kuma ba lallai CBN ta dauki matakin da ya dace ba, tunda dama sun fito da wannan hanya ne domin a boye mummunan satar dukiyar Kasa da akayi
Duk wanda yake da hannu a wannan zaluncin Allah Ka isar mana tsakanin mu da shi
Tags:
Labàrin wasann