Shugaba Buhari yace bai ga dalilin yan Nijeriya na ƙorafi a kan canjin Kudi ba !!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Yace an baiwa yan Nijeriya wata uku cur, tun daga October har zuwa Junairu kan su mai da kudadensu Bankuna, a tsawon wannan lokacin ko nawa kake da shi ya ci ace ka mai da su Banki.


Yace babu gudu ba ja da baya game da canjin kudin, da kuma wa'adin da gwamnatinsa ta bada ta hannun babban Bankin Kasa (CBN) na dena amsar tsofaffin takardun kudi.


Kamar yadda shugaban ya faɗi da harshen Turanci; "There's no goyin Bek!"


A safiyar yau Litini a yankin da nake na lura al'umma sun fara ganin sakamakon canjin kudin, a yayin da Shaguna da dama suka dena amsar tsohon kudi duk da cewa mutane basu da sababbin, kuma da dama basu da account din Banki. Idan ma suna da account din ta yaya za ka sayi kayan Naira 300 ka tura ta Banki, alhali za a cire maka charges daban-daban mafi karanci 53? Sai ma in mai kayan na da Asusun.


Kai, in ka yi transfer ma don za ka sayi kaya ai sai mai kaya ya ga 'alert' sannan ya baka kayan ka tafi ko? To a kwanakin nan abin ya kara cabewa, sai a tura kudi su yi awowi ko su kwana su yini kafin su isa ga wanda aka turawa. 


Don haka masu abincin saidawa da dama basu fito ba saboda ba zai yiwu su sai da abincin a basu tsofaffin kudi ba, sun hakura da sana'ar zuwa abin da hali ya bada. Haka ma sauran harkoki.


Wasu na cewa wannan kila shine faɗan karshe tsakanin baban talakawa da mutanensa a yayin da wa'adin mulkinsa ke shirin karewa. A yayin da yan amutun tsohon wadanda a kan same su misalin 1 a cikin dubun mutane, suna fatan Kaka Bola ya maye gurbin Babansu, saboda ko ba komai an san tsofaffi musamman kakanni da jinkai da son jikoki.


Tun bayan kisan Kiyashin fiye da mutum dubu daya da sojojin Baba suka yi a kan Musulmi a Zariya a watan Disambar 2015, ba a samu wani abu da labarinsa ya game kowa a Nijeriya kamar canjin kudin nan ba.


Ko da yake da daman mutane Kisan kan da sojojin tsoho suka yi suna ganin daidai ne tunda kan mutanen da ba fahimtarsu daya bane, kamar dama Baba ya rage musu aiki ne. Shi kuwa wannan canjin kudin na Baba ba Shi'a ko Sunnah, ko Darika ko Izala ko Kirista ko marasa addini kawai ya taba ba, har kaji da akuyoyi sai sun shaide shi. Dama zalunci girma da fadi yake yi idan ya samu shimfida. 


Ina ganin kamar akwai sauran abin ƙeta da muguntan da Buhari zai yi kafin ya sauka a mulkin nan, wanda da shi ne zai tabbata har ga mutane masu tunanin dabbobi cewa shi tantirin matsiyaci ne. Sai dai Allah Ya ba kowa hakuri shigen wanda Ya bamu lokacin da Buhari ya kashe masoyanmu ya bizne su a rami guda, ya kama Jagoranmu ya tsare tsawon kusan shekara 6 a Kurkuku.


Allah Ya rangwanta mana. Ya mana maganin azzalumai.


— Saifullahi M Kabir

23/01/2023.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post