Shirya Maulidin Annabi Da Sayyida Fatima Ne Sirri Da Ijabar Kasuwancina, -'Yar Kasuwa, Malama Zaliha Muhammad Katsina.......!!!

 




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Daga Mohammad A. Isa.


Malama Zaliha Muhammad daya ce daga cikin 'yan'uwa mata 'yan kasuwa Almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky(H) da ke Da'irar Katsina, wadda duk shekara take shirya gagarumin Maulidin Manzon Allah da Sayyida Fatima(S.A). Kamar kowace shekara, bana ma ta shirya Maulidin, sai dai a wannan shekarar ta yi amfani da wani salo ne sa6anin na shekarun baya; tayadda ta raba danyen abinci a wajen Maulidin na bana, wanda ta rarraba wa daidaikun mutane mabukata da suka hada da; Marayu, Iyalan 'yan'uwan da suka rasu, Fudiyyoyi da kuma wasu ba'alin Malaman Makarantun Islamiyyu. Bayan kammala taron Maulidin, Wakilin Thurayyah Media Trust, Mohammad A. Isa, ya zanta da ita dangane da wannan tagwayen Maulidodi da ta sake shiryawa a bana, da yadda ta canja salon maulidin a wannan shekara inda ta zabi ta raba danyen abincin ga mabuka. Ga yadda firar tasu ta kasance:


THMT: Za mu so ki bayyanawa mai karatu sunanki.


Malama Zaliha Muhammad: Sunana Zaliha Muhammad wadda aka fi sani da 'Mai Kuka'.


THMT: Ga shi a bana ma kin shirya wannan maulidi da kika saba shiryawa kuma ya zo a daidai farkon watan Rabius-thani, wane sako kike da shi ga mai karatu kan wannan maulidi?


Malama Zaliha Muhammad: Alhamdulillahi. Ina mika godiyata ga Allah(SWT). Ina shirya maulidin Sayyida Fatimatuzzahra tun wajen 2007. Kuma Alhamdulillahi daga lokacin da aka ce Maulidin Manzo ya zo da na sayyida Zahara(S.A), to idan ban samu na shirya wannan maulidi ba gaskiya ni kan ji ni ban samun natsuwa, domin gaskiyar lamari wannan shi ne sirrin rayuwata. Saboda da zarar na cire wani abu daga cikin yankin arzikina wanda Allah ya yi min( a kasuwancina), to ni kan ga abin ya lillinku, linkuwar ma da ta wuce hankali. Saboda haka gaskiya ina jan hankali ga 'yan'uwa ba ma ga Burazu ba har ga Sisters su rika shirya Maulidin Sayyida Zahara(S.A) domin ya kan gusarwa da mutum talauci kowane iri, da duk wata matsala da ta damu mutum, Allah ya kan kawo mai daukin ta. Idan mutum ya yi tawassuli da dan abin da zai cire ko ya yake, ko da kau da 'Pure water' ne, zai ga budi a cikin arzikin nasa. Saboda ni na fara shirya maulidin Sayyida Fatima(S.A) da 'Pure Water' leda daya ne tal. Saboda haka ina kira ga 'yan'uwa Musulmi da su rika gwada yin hakan su ma.


THMT: Maulidin nan da kike shiryawa duk shekara tsawon kimanin shekaru sha-biyar kenan daga shekarar 2007 da kika ce zuwa yau, shin Maulidin Manzo ne kike shiryawa kadai ko na Sayyida Fatima; rarraba su kike yi daban-daban ko kuma hade su kike yi, ko ya abin yake?


Malama Zaliha Muhammad: To, gaskiya ni na Sayyida Zahara da na Manzo(S) ne nake hadewa duka in yi. Ban taba warewa daban-daban ba. Duka nake hada su. Idan na baro lokutan watan Rabiul-Awwal, sai in gangaro watan Sayyida Zahara(S.A) kawai sai in hade in yi su gaba daya. Ba ni kan ware daban-daban ba.


THMT: Wannan Maulidi da kika shirya na bana kamar ya sha bambam da na sauran shekarun baya duba da buhunnan abinci da kika rarraba, ya akai haka?


Malama Zaliha Muhammad: To, gaskiya alhamdulillahi. Yanayin yadda na samu kaina da dan abin da yake hannuna, to na kan godewa Allah in ware wani abu in sadukar da shi saboda sayyida Zahara(S). Sayyid (H) ya ce mana; idan ka cire kwano daya na Gero ka ba wa bawan Allah wanda yake cikin yanayi na jarabawa, kowace kwaya daya (ta Geron) a kan ware maka ladarta daban. To shiyasa kowace shekara na kan yi la'akari da halin da 'yan'uwa musulmi suke ciki, ba ma almajiran Malam Zakzaky(H) ba, har ma wadanda ke wajen harkar nan na kan yi kokari in ware wani abu in sadaukar da shi saboda ya zama Hirzi a wurina. Yanzu ka ga yanayi muke ciki na talauci da matsi, wani abin da zai ci ma babu, sai na ga bari in can tsari, sai na tanadi kayan abincj na ba su. Kuma akwai 'yan'uwanmu almajiran Malam Zakzaky(H) wadanda su ba shahada suka yi ba (sun rasu), amma 'ya'yayensu da suka bari saboda yanayi na matsi, ya kansa har ma kamar mun mance da halin da suke ciki. To ka ga wajibi ne a kanmu mu rika tunawa da halin da irin wadannan Burazu suka bar Iyalansu. Saboda kai ma, ko ni ma, ko ke ma in ka tafi ka bar naka kana so a tallafa masu. To wannan abin da za ka dan ware ka ba su ko yaya yake duk da ba zai iya dauke masu daukacin radadin halin da suke ciki ba, amma ko da kwana daya ko biyu ne ya dan kwakkwafa su, su kan ji dadi, sai ka ga ana ta harkoki da su. Amma sai ka ga wani lokaci mun dan yi shiru. Sai ka ga Buraza ko Sista sun rasu sun bar su 'ya'yayensu amma sai ya zama kamar mun manta da su. Ya kamata fa mu rika tunawa da cewa wannan fa dan Buraza ne. To ire-iren irin wadannan, ina jan hankali ga su 'yan'uwa mu maida hankali gare su walau a daidaikunmu ne, a mu biyu ne, a mu Uku ne, Sista ce, Buraza ne mu yi kokari mu rika kula wadannan gidajen.


THMT: Baya ga so da kaunar Manzon Allah da Sayyida Zahara(S.A) da ya sa kike shirya Maulidinsu duk shekara a lokaci guda, akwai wasu sirruka ko Ijabobi da wala'alla za ki iya fadawa mai karatu ko ba komi don kwaitarwa?


Malama Zaliha Muhammad: To, a gaskiya ni shirya Maulidin manzo da iyalan gidansa yana daya daga cikin sirrina da ijabata. Ba ni da wani abu da zan iya ce maka takamaimai na rike illa baicin wannan. Kuma in na ga wasu matsaloli a cikin kasuwancina ko wasu lamurrana, to na kan shirya maulidi sai in yi kamun kafa da tawassuli da Iyalan Manzo(S), kuma a gaskiya a lokacin sai in ga matsalolin sun janye kuma shi kasuwancin ya daukaka yadda ba a tunani. Wannan shi ne sirrin kawai.


THMT: A jawabin godiya ga mahalarta wannan Maulidi da kika yi, sai na ji kin ce kin sadaukar da ladar wannan Maulidin zuwa ga Sayyeed Zakzaky(H) ko?


Malama Zaliha Muhammad: Eh tabbas! Malam Zakzaky(H) mun yi masa alkawali za mu ba da ranmu, jininmu, dukiyoyinmu da dukkan abin da Allah(T) ya yi mana arzikinsa. Saboda haka, babu wani abin da za mu tanada mu ce mun ware shi namu ne (mu kadai), a'a mu kan ware wani abu mu ce Allah kai mana shaida ka kai ladar komin yawanta a wajen Malam Zakzaky(H). Domin mu albarkacinsa muke ci, kuma shi ne mafitarmu, shi ne mahangarmu kuma shi ne majinginarmu a ranar alkiyama.


THMT: Wane kira kike da shi ga 'yan'uwa Almajiran Malam Zakzaky(H) da kuma sauran al'ummar Musulmi baki daya dangane shirya irin wannan Maulidi na Iyalan Annabi(S)?


Malama Zaliha Muhammad: To Alhamdullhi. 'Yan'uwa musulmi musamman Sistoci 'yan'uwana; su yi kokari su samu ko mutum biyu ko ma mutum daya ne su hadu, ko da naira goma naira ashirin ne su rika ajewa da sunan tarin kudaden shirya maulidin Sayyida Fatuzzahra(S).Musamman ita da muke ke cewa muna koyi da ita. Ko ita kadai ce ka zaba kana shirya maulidinta, to kana kamar kana shirya na Annabi(S) ne da sauran iyalan Annabi baki daya.. Sannan su kuma sauran mutane, to su ma sai in ce kawai su rika shirya maulidodin saboda Fatimatuzzahra(S). Mu kuma ba ka da wani abu da za mu iya fadi wanda zai nuna maka tsantsar son da muke wa sayyida Fatimatuzzahra. Duk abin da za mu fadi ko mu aikata na son sayyida Zahara(S.A) ko kaunarta ko wani aiki, to mun gaza, ba mu iya ba. Kawai dai muna kamun kafa ne da su Malam Zakzaky(H) su suka san sayyida Zahara(S.A), amma mu gaskiya ba mu san ta ba.


THMT: Malama mun gode.


Malama Zaliha Muhammad: Ni ma na gode. Allah ya kar6a mana!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post