Shaikh Abduljabbar: Katimi a gaba Katurmuji (III)...

 



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 




ALKALAMI KA FI REZA KAIFI


Tate da M. I. GAMAWA




Wani abin lura shi ne, masu kare makiya Annabi na hakika har yanzu ba su ce komai ba, don sun san Shaikh Abduljabbar ba makiyin Manzon Allah ba ne. Haka su ma masoya Annabi ba su yi murnar hukuncin da Alkali Yola ya yanke wa Shaikh Abduljabbar ba. 


Da Yammacin Duniya sun san cewa da gaske Shaikh ya yi batanci ga Manzo, tabbas da an same su a sahun gaba wajen Allah wadai da hukuncin Alkali Yola, amma sun yi shiru, sun yi kamar ba su ji labarin hukuncin ba. Yammacin Duniya sune suke bai wa duk ayyanannen makiyin Annabi mafaka da kariya a kasashensu, kama daga Salman Rushudi, Chioma Daniel zuwa duk wadanda yanzu haka suke holewa a Turai da sunan samun mafaka. Ba su fasa ba, kuma ba sa gajiya wajen ba da mafaka ga makamantan wadanda muka ambata a sama. 


Tabbas da Shaikh mai batanci ne, da yanzu sun yi wa gwamnatin Kano da Najeriya hujumin da dole Shugaban kasa ya sa baki don gudun takunkumin karya tattalin arziki. Amma hukuncin Shaikh Abduljabbar bai ba su wata damuwa ba. Domin sun san shi mai kare Annabi ne aka yi wa fin karfi ta hanyar Ganduje, Gwamnan Kano. Tabbas Alkali Yola bai koyi darasi daga abin da ya samu dan unguwarsu, Marigayi kuliya Alkali da Shaikh Nasiru Kabara ya tsinewa ba. Ya kamata Alkali Yola ya tuna yadda rayuwar kuliya Alkali ta kare don koyon darasi. 


Wani abin takaici game da wannan hukunci shi ne, wasu sassa na hukuncin da suka hada da, hana lika hoton Shaikh Abduljabbar a ko’ina a fadin Jihar Kano, haka kuma sauraron wa'azinsa ko a cikin gida balle a mota. Wannan wauta ta yi yawa. Ban san wanda ya fi kowa aikata wa Najeriyawa mugun laifi ba. Shin Manjo Chukuma Kaduna Nzeogwu ne, wanda ya yi juyin mulkin da ya tafi da rayukan Sardauna da Tafawa Balewa ko Laftanar Kanar Bukar Suka Dimka ne, wanda ya yi juyin mulkin da ya lakume Janar Murtala ko Kanar Odumegu Ojukwu, wanda taurin kansa ya haddasa yakin basasan da ya jawo salwantar rayuka masu yawa? 


Shin cikin su akwai wanda aka hana sa hotonsa a fadin kasar nan? Ba don waninsu ya kai darajar farcen Manzon Allah ba, amma tabbas sun fi Manzo gata a gun dokokin Najeriya. Duk da girman wadanda suka kashe, babu inda wata kotu ta ba da hukuncin hukunta wanda ya lika hotunansu a gidansa ko shagonsa ko wani waje a fadin Arewa ko Najeriya. Wannan shi ma wani nau'in Fir'aunanci ne da ya kamata ya tafi da tafiyar Fir'aunan Misira. 


Bari mu leka mu ga abin da wasu ke cewa babu a littafan Ahlussunna. Shin babu inda aka ce Manzo ya yi fitsari a tsaye a kan Bola ne? Shin babu inda aka ce yana zuwa wajen matar wani, ya dora kansa a cinyarta, tana duba masa kwarkwata ne? Babu inda aka ce yana zagin Sahabbansa babu gaira babu dalili ne? Shin babu inda aka ce ya shiga garin Khaibar ba tare da ya suturta kansa ba ne? Babu inda aka ce wata mata ta nuna tana son sa ya ce ta je wani waje mai duhu ta jira shi, kuma ya tafi ya biya mata bukatarta ne? Babu inda aka ce yana tsere da matarsa a kan Titi? Babu inda aka ce ya yi wa Sahabbansa tayin kwana a daki daya, alhali yana tare da matarsa a cikin dakin? Shin babu inda aka ce yana sumbantan alkalamin jikansa? 


Wadannan kadan ke nan daga abubuwan da Annabin Ahlissunna yake aikatawa, amma a yau babu mabiyinsa da yake so a alakanta shi da irin wadannan ayyuka, duk da cewa sun gani a rubuce cikin Alkur'ani cewa "Abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike." Sau nawa aka tube limamai kan aikata daya daga cikin ayyukan da muka ambata a sama? Me ya sa al'ummar Musulmai ta mai da duk wadannan ayyuka abin ki kuma take hukunta duk wanda ke yin su ko dai a kotu ko mutane su kyamace shi? Me ya sa ayyukan "Annabi" suka zama abin kyama ga al'ummarsa? Wane irin al'umma ce, ko kuma wane irin Annabi ne haka?


A cikin shekarun saba'inoni, wasu wadanda ba Musulmi ba sun rubuta wani littafi da Turanci mai suna "Who is this Allah?" Wanda aka sa sunan wani wai shi "Moshe" a matsayin Mawallafin littafin. Cikin Littafin babu abin da ba a yi ba na goranta wa Musulmi da irin wadannan rubabbun hadisan. A cikin wannan yanki na arewacin Najeriya, wani Malamin Coci, wato Rabaran ya ga wasu Musulmi na kiran abokinsu Arne, Rabaran ya tambaye su don me suka kira shi Arne ko Kafiri? Sai suka ce masa don yana fitsari a tsaye. Sai ya ce musu "Da a ce akwai Malamin Musulunci a cikin ku, da na fada masa inda aka rubuta a cikin littafanku, ba daya, ba biyu ba, cewa Annabinku yana fitsari a tsaye, kamar yadda abokinku ya yi." Yara suka koma gida suna mamaki. 


Wadannan kidahumai masu kare zantukan banza da suka zo a cikin "Sahihai" ba su san cewa akwai wadanda ba Musulmi ba, amma sun karanci Musulunci sosai. Ba ma tarihin Musulunci ba, shi Musuluncin kansa. Karamin misali shi ne an yi shekaru masu yawa Kirista yana jagorantar tsangayar koyar da Addinin Musulunci a Jami'ar Jihar Legas, wacce ake kiranta LASU a takaice. Shi Kirista ne ya yi karatun Musulunci a kasashen Musulmi da suka hada da Misira har ya samu PHD. Me za ka boye masa a Musulunci? 


A shekarun baya akwai wani Rabaran da ya fassara Risala ta Abu Zaid Kirawani daga Larabci zuwa Turanci, har ma ya kai wa marigayi tsohon Grand Khadin Jihar Neja Shaikh Ahmad Lemu domin ya yi masa ’yan gyare-gyare. Yanzu haka akwai littafin a kasuwa. Kafin Yusuf Ali ya fassara Alkur'ani mai girma, wasu wadanda ba Musulmi ba sun fassara shi. Shin su ma za a iya boye musu wannan kwamacalar da ke cikin wadannan hadisai da ake kira Sahihai ne? 


Tabbas! Duk yadda Musulmi suka nufa, kifi na ganin su, domin komarsu ja ce. Ba Musulmi kadai ke karanta littafan Musulunci ba, duk abin da aka rubuta da sunan Musulunci yana nan a kasuwa, don masu kudin saye, kundin nan, kuma yana hannun Musulmi da wanda ba Musulmi ba, bil hasalima wadanda ba Musulmi ba, su suka fi Musulmi kudi a Duniyar yau. 


Za mu ci gaba insha Allah.

Mun ciro daga Almizan ta 1575 Juma'a 13 ga Jimada Thani, 1444



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post