[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
wani abin da wasu yan uwa basu sani ba gameda Sayyid Zakzaky (H) shine
shi Sayyid H) baya aiwatar da wani abu ko daukan mataki cikin harka har sai ya nemi irshadi daga sama
wani ɗan misali
a shekarar 2010 ina cikin waɗanda ake zama dasu don ganin an shirya mu'utamar a yankin yarbawa
sai aka nemi irshadin su Sayyid (H) akan wani gari ne yadace ya yazama inda za a gudanar tsakanin Legas ko Ibadan ko Ilori?
sai Su Sayyid H) suka ce abasu lokaci sai sun shiga HALWA tukuna
bayan fitowar su daga halwar suka ce a Ilori za a yi insha Allah
don haka idan kana son sanin wane ne wannan saman da yake wa Sayyid Zakzaky (H) irshadin?
sai ka koma cikin wasu jawaban su Sayyid H) guda uku zaka samu amsar ka
sune
1 cikin wani jawabi sa kafin waqiya akwai inda su Sayyid (H) ke cewa mu muna da shugaba mun san shi ya san mu
2 cikin wasu Jawaban da yake bada qissar Sheikh Isa Arrummaniy da yanda yashiga HALWA yasamu ganawa da Imamul Hujja af
sai su Imam suka warware musu wata shubuhar da wani dan sunan yashirya don yaudarar musulmin baharain
3 cikin jawabin Jagora na nisfu sha'aban da yagabata bara
inda suke cewa👇
"To, amma har yanzu Sahibul Asr Waz Zaman (AS) ne ke tafiyar da abubuwa. Na sha fadin wannan cewa, su fa Shi’a ba suna jiran Mahdi ya zo ne su bi shi ba,
su shi suke bi yanzu din nan ma. Ka san akwai masu tunanin Mahdi zai bayyana, in ya bayyana za a bi shi. To mu shi muke bi yanzu. Kuma yana nan tare da mu. Shi ke kwakkwafa al’amura."
— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a jawabinsa na Nisf Sha'aban 1443
don haka idan ka fahimci wannan yaren to zaka sallama wa matakan da Sayyid Zakzaky H) suke dauka tun kafin waqiya da bayan fitowar su.