Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ceto yara biyu tare da kama wadanda suka yi garkuwa da su




A ranar 26 ga Janairun 2023 ne wasu magidanta biyu, Isyaku Salisu da Auwal Sale, dukkan su mazaunan Bachirawa da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano suka shigar da rahoto ga rundunar 'yan sandan jihar Kano cewa yaransu masu suna Umar Isyaku da Aliyu Auwal masu shekaru 3 da 4 bi da bi, an yi garkuwa da su, kuma an rubuto masu wasika tare da neman su biya kudin fansa miliyan ashirin, daga  baya masu garkuwar suka yi ragi zuwa naira miliyan biyu.


To sai dai bayan samun rahoton, kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Mamman Dauda tare da hadin gwiwar SP Muhammad, wanda  shi ke  shugabantar rundunar yaki da garkuwa da mutane tare da tawagar shi sun ceto yaran sun kuma yi nasarar kama batagarin.


Nura Auwal da Abubakar Lawal, 'yan shekarar 22 da haihuwa da ake  zargi da aikata wannan laifi tuni suka amsa laifinsu na hada kai wajen yin garkuwa da yaran domin neman kudin fansa bayan da suka shiga  hannu yayin da aka fara gudanar da bincike cikin al'amarin.


 Ana dai sa ran ba da dadewa ba za a kai su kotu domin fuskantar hukunci bayan kammala  bincike. 


Duk da cewa yaran da aka ceto din a cikin wani kangon gini suke, to amma ba wata cutuwa a tare da su.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post