[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Waní rikicín da ké da alaƙa da Limancí ya haifar da rashìn iyúwar Sallar Juma'a a wànnan rana a Masallacín Juma'a na Darul Hadis da ke Unguwar Tudun Yóla a Jìhar Kanó.
Masallacin wanda marigayi Dakta Ahmad BUK ya ke Limanci ada, hayaniya ta ɓarke cikinsa ne a daidai lokacin da sabon Limamin Masallacin ke ƙoƙarin hawa mumbarin Huɗuba amma mabiya tsohon limamin su ka janyo shi inda hakan ya haifar da hatsaniya a masallacin.
Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito cewa tuní an rufé masallacin tare da baza jami'an tsaro inda ɓangarorin biyu su ka ɗunguma zuwa ofishin ƴan sanda na Bomfai domin sasanci, kuma tuni lamura sun fara lafawa a can masallacin.
Tags:
Labaran Duniya
Karamar mallam Abdoul jabbar mujaddadi
ReplyDelete