DUK MATAR DA BA TA RIKE WADANNAN ABABEN BA
ZATA RASA RUWAN MAMA BA BAYAN HAIHUWA.
Matsalar RUWAN mama Yana daga cikin Abunda
yake jefa Mata Masu jego cikin tunani da rashin
tabbas daga karshe a fada neme nemen
magungunan RUWAN mama ko ayita Dora laifi ga
Maijego. To ga hanyoyi 5 da ake anfani dasu Dan
Samar da RUWAN mama cikin lokaci.
1- Bayar Da Maman da zaran an haihu, Azama ko
kokarin Bayar da mama akaran farko Yana tabbatar
da zuwan ko gangarowar RUWAN mama, Sannan
hakura jinjiri ya saki mama da kansa ba Yana Sha
Ana kwacewa ba. Duk yanda Maigida ke bukatan
Maijego Yana wa Allah ya bari jariri ya koshi ,
ke hajiya kada ciniki yasa kina Anshe mama daga
Jinjiri alhali ba koshi ba.
2- Matsa Mamuna, lokacin da yaro keshan mama
akwai bukatan Uwa ta Kama Maman tana Dan
pumping dinsu a hankali wannan Yana taimakawa
wajen tattara RUWAN mama ta yanda yaro zai koshi
da sauri.
3- Bayar da Mama daga kowane bangare, Idan aka
fara bada mama a tabbatar da Yaro yasha kowane
lokaci daya, ba wai a bada na Dama ba a bari
hakanan sai anjima a bada na hagu wannan
ragguwar dabia ce kuma tana Bata mama ta yanda
mu kanmu sukan daina bamu sha'awa, da Allah ki
dubi Kona Awakinki idan Dan akuya nashan mama
daya ya dayan ke kasancewa.
4- Anfani da Wasu magunguna, Supplements da
sauran Sanadaran da zasu iya taimakawa.
5- Zaman mace Mai shayarwa, Wannan Matsayin
Yana ankarar da mace na mantuwa daba yaro
mama lokacin daya dace, koda Bata tare da yaron
da zaran lokacin shansa yayi zata tina tofa ita Mai
shayarwa ce.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group din mu na Telegram Anan
👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/
DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com