[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Manyan Masana Halayyar Dan Adam na ganin cewa Shiryuwa da Gyaruwar kowacce Al-umma, yana hade ne da Shiryuwa da Gyaruwar Matan wannan Al-mmar.
Karfin kudurar mace da Tasirin Ikonta ya kai matsayin ita kadai tana iya daukar nauyin yiwa Al-umma sukutum kyautar Guzurin da zai kaisu ga Kamala da Daukaka, ya Janyo masu ci gaba. Ta hanyar Reno da Tarbiyar Diya na Gari, wadanda sanadiyyar wannan Renon za su ceto Al-ummarsu daga wannan Kunci.
To haka idan Mace Lalatatta ce, tana iya Lalata Al-umma gabaki Daya.
Wannan Daya ce daga cikin Sirrukanda suka sa Allah mai Girma ya yiwa Annabin Rahama Kyauta da Sayyida Fadima, a Matsayin wadda ta Gajeshi. Sabanin ssauran Annabawa, yana dunkule ne a cikin wannan Nuqdar.
Sayyida Fatima itace Uwa mai Renon wannan Al-umma. Wadda ta Reni Taurari guda biyu, ta kula da Babansu Sarkin Muminai, ta cikasu da Guzuri domin wannan Al-umma ta zamo mafi Al-khairi.
Amma sai Al-ummar ta watsa masu Kasa a Idanu, ko ambaton Sunayensu bata so, balle ayi maganar basu dama, su koyawa Duniya abunda su ka Gada daga Uwar Sharifai.
Duk wata Musiba da take samun wannan Al-ummar tanada Alaqa ta Kai Tsaye ko ta hanyar Sababi da rashin daukar Irshadin Sayyida Fadima bayan Wafatin Manzon Tsira.
Muna godewa Allah da ya sa muka san wannan Haske,muke Kauna da Begen wannan Tsarki, muke yada zantukan wannan Gida, wanda shi Kadai ne Gida.
Muna Godewa Allah da ya bamu Allamah Sayyid Al-zakzaky, wanda shi ne ya haska wannan Lamari a wannan Nahiya, ya Kakkabewa Tafiyar Ahlu baiti Kura, Kaunarsu da Biyayya garesu ta dawo Sabuwa.
Happy Zahra Day Masoya
Shamsudeen Hassan