A ranar Talatar ne za’a bude “Largest Vertically Intergrated Petrochemical Complex Refinery” in the World, wato Matatar mai mafi girma a jerin irin ta a duniya, wanda aka yi wa suna da “Dangote Refinery” wanda duk duniya babu irin wannan Refinery a tsarin irin ta wajen girma da zuba Na’urorin aiki mafi karfi a duniya.
~ Yanzu haka an kammala ginin ta da komai da komai a yankin “Lekki Free Zone” dake kusa da birnin Lagos.
Wannan Matatar zata dinga tace Gangan Mai Lita dubu Dari 650,000 a kowace rana.
~ Wani babban abun burgewa shine Kai tsaye za’a dinga jawo Man Fetir din da Gas daga Yankin Nigeria Delta zuwa Dangote Refinery, already tuntuni an Gina hanyoyin da ‘danyen Man zai bi yaje Refinery din tare da Iskar Gas din, ba Motoci ko jiragen ruwa ne zasu dinga kaiwa ba.
~ Wannan zai yi matukan rage Fasa Bututun Mai (Gas Pipelines) da ‘yan Ta’adda suke yi.
Haka Kuma Matatar zata samar da aiyukan yi Kai tsaye (Direct Job) wa mutane dubu 4,000, zata samar da aiyukan yi daga gefe (indirect job) wa mutane dubu 145,000.
~ Wani babban abun burgewa na biyu shine, Matatar Man zata dinga siyarwa kasashen duniya da Man ne da kudin Nigeria Naira, dukkan kasashen da zasu zo Nigeria domin Sayan man dole su nemi Naira.
~ Wanda hakan zai taimaka wajen daga darajar Naira a duniya, da Kuma dawo da hauhawar tsadar kayan Masarufi kasa.
~ Babban abinda Matatar zata yi da kowa zai Gani a zahiri shine dawo da farashin Man Fetur baya, saboda yanzu Nigeria zata daina shigo Man Fetir daga kasashen duniya da kaso sama da Sittin. Kuma gwamnati zata daina ko zata rage kaso Mai dimbin yawa na kudaden da take kashewa akan Oil subsidy, wato tallafin Man da ake shigowa dasu Nigeria.
~ Tallafi ne da ake asarar Trillion of Naira a duk shekara, Wanda baya amfanar talakawan da ake yi domin su.
~ Shigo da Man a kasar da take da arzikin Man Kuma Bata iya tace koda ‘daya bisa goman abinda take bukata a Rana shine babban dalilin tsadar Man a kasar, wannan tsadar zata zama tarihi in Sha Allah a nan kusa.
~ Wannan Matatar zata dinga ajiyewa Nigeria ribar kudi har Tsaban Dala Biliyan Goma Sha daya (Kimanin Naira Trillion Takwas).
~ Haka Kuma a kowace rana Matatar zata dinga samar da 3 Billion Standard Cubic Feet of Gas (Daily)
~ Wani Babban aikin Kuma shine:
~ Matatar zata dinga samar da tataccen Man Fetur Lita Miliyan 65 a duk Rana. Kuma zata dinga karban ‘danyen Man Fetir daga kasashen waje tana tace musu bayan ta tace na Nigeria, shigowa da Man kasashen waje zuwa cikin Nigeria zai yi Generating Biliyoyin kudade wa kasar a duk wata da duk shekara.
~ Bayan wannan a kowace rana Matatar zata dinga samar da 15 Million Liters of Diesel sai Kuma Man da ake zubawa Jiragen sama wato “Jet Oil” Lita Miliyan hudu.
~ Kasashen duniya da dama ne suke rububin shigowa Nigeria domin ribatar wannan babban alkhairi, kasashen dake Africa da dama zasu daina kaiwan Man Fetir din su kasashen Turai zasu karkato su dawo Nigeria.
~ An kashe Tsaban kudi Dala Biliyan $19 domin Gina wannan Matatar.
A cikin kudin, gamayyar Bankunan ciki da wajen Nigeria sun zuba Dala Biliyan uku da Rabi.
Ranar Talatar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai Bude wannan Matatar, wacce Kuma zata samar da wutar lantarki me yawan gaske ga kamfanonin Nigeria dama kasar Baki daya.
~ Matatar zata yi sanadin saukowar farashin kudin hawan jirage a cikin Nigeria (Domestic Flights) wanda yayi tsada.
Sauran bayanai suna tafe nan gaba game da wannan babban alkhairi da ya tunkaro Nigeria, Africa da ma duniya gaba daya.
~ Wannan ba karamar dama bace ga Nigeria kasar da take da 37 Billion Oil Barrel Reserve.
Kaso 65 na Ma’aikatan da za’a dauka a Matatar ‘yan Nigeria ne.
~ Musamman a yanzu da aka fara hako man Fetir a jihar Bauchi da Gombe, da kuma kokarin hakowa a jihar Sokoto da Benue, Allah ya sakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da alkhairi bisa ga haka, da Kuma Alhaji Aliko Dangote da wannan kishi da suka nuna wa kasar da jama’a kasar. Kamar yadda Malam Abdul-Hadi Isah Ibrahim.ya rawaito.