@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE.
- Dr. Naziru Umar Muhammad.....✍️
Nawa ne nauyin jakar da ya kamata yaro ya riƙa ratayawa domin kiyaye ciwon jiki?
Wannan amsa na nan cikin shawarwari takwas ga iyaye da malamai game da rataya jakar makaranta.
Duk da muhimmancin jakar makaranta ga ɗalibi, kulawa da lafiyarsa ma na da muhimmancin gaske. Sau da yawa, ƙorafe-ƙorafen yara 'yan makaranta kan matsananciyar gajiya, ciwon baya, wuya ko kafaɗu na da alaƙa da ɗabi'ar nan ta rataya jakar makaranta maƙare da littafai, kayan rubutu, abinci ko abinsha, wani lokacin ma har da sauran kayayyakin da ba a buƙatarsu a makaranta.
Bugu da ƙari, bincike ya nuna yadda rataya jaka mai nauyi ke sauya lafiyar numfashi saboda yadda nauyin jakar ke takura haƙarƙari da huhu.
Haka nan, masana lafiyar ƙashin gadon baya sun ja hankalin iyaye da malamai cewa lafta wa yara jakankuna masu nauyin gaske na da gagarumar illa ga lafiyar yaran.
Shawarwari takwas domin kiyayewa:
1) A tabbatar nauyin jakar baya ba ta wuce kaso goma zuwa sha biyar cikin ɗari(10 - 15%) na nauyin yaro ba. Nauyin jakar bayan da ya wuce kaso goma zuwa sha biyar cikin ɗari(10 - 15%) na nauyin yaro zai riƙa rinjayar yaro wanda hakan kan sa yaro durƙusawa ko sunkuyawa gaba domin kar nauyin jakar ya rinjaye shi.
Misali, idan nauyin yaro ya kai kilogiram talatin (30Kg) a kan ma'aunin nauyi; to nauyin jakar da ya kamata ta ɗinga ratayawa zai yi dai-dai ne da kilogiram uku zuwa uku da rabi (3 - 3.5Kg).
2) A yayin da aka goya jakar baya, ba a son ta sauko ko ta zarce fiye da farkon ƙashin ƙugu, ko kuma sama da maɗaurin wando kaɗan.
3) A zaɓi jaka mai aljihuna; a sanya abin da ke da tsini ko kaifi a aljihu mafi nesa da gadon baya. Sannan a sanya kayan da ke da nauyi a aljihu mafi kusa da gadon baya.
4) Lafta wa yara littattafai a cikin jakar makarantarsu ba dole ba ne. Girman jakar makaranta fiye da ƙima kan sanya yara ɗaukar kayayyaki masu nauyi da ba a buƙatarsu a makaranta.
5) A umarci yaro da rataya maratayan jakar biyu a kafaɗunsa na hagu da dama kowane lokaci. Domin sanya maratayin jakar a kafaɗa ɗaya kawai zai kawo rinjayar nauyin zuwa ɓari ɗaya; wanda hakan kan kawo ciwon wuya, kafaɗa, baya da kuma tasgaɗewar ƙashin gadon baya yau da gobe.
6) A zaɓi maratayin jaka mai faɗi kuma mai taushi; domin siririn maratayin jaka na iya nitsewa cikin kafaɗa har ya ci wa yaro jiki.
7) A zaɓi jaka mai maratayan da za a iya ƙarawa ko ragewa dai-dai da tsayin yaro. Domin maratayan jakar da ba za a iya rage su ba na iya kawo zarcewar ko taruwar nauyin jakar zuwa inda ba a buƙatarsa a gadon baya.
8) Idan jakar yaro ta yi nauyi sosai, a shawarci malamansa domin rage littattafan da za a iya barin su a makaranta domin rage nauyin dakon littattafan daga gida zuwa makaranta kullum.
A yayin da yaro ya fara ƙorafin matsananciyar gajiya, ciwon baya, wuya ko kafaɗu, tuntuɓi likitan fisiyo domin neman shawarwari da kuma magance ƙorafe-ƙorafen.
By Doctor Naziru Umar Muhammad...✍️
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group din mu na Telegram Anan
👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/
DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com