Muzaharar Maulud Sayyada Fatima (A's)Ta Katsina Ta Kayatar.

 



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 




Daga Moh'd A. Isa.


Kamar sauran garuruwa, 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) na katsina, su ma sun bi sahun takwarorinsu wajen gudanar da Muzaharar Maulidin Sayyida Fatima(S.A) a ranar Lahadin nan.


Muzaharar wadda ta soma motsawa da misalin karfe 10:00 na safe, ta tashi ne daga Unguwar Madawaki ta yo Babban Masallacin juma'a, ta karya kwana ta bi ta Babban Ofishin 'Yan Sanda (CPS), ta sake karyawa ta mike Titin kofar Guga, ta kuma kara karyawa ta bi ta Kasuwar Filin Bugu, ta mike dodar zuwa Titin Rafin dadi, a yayin da ta karya ta mike kan Titin Gwabron gida, ta sake karyawa ta bi Titin zuwa Kofar kwaya, inda ta tuke a Filin tsohuwar Makarantar ATC.


A yayin muzaharar, 'yan'uwa Mata, Yara da Matasa, sun fito fes-fes da sabbin kaya rike da Tutoci, a yayin da wasu ke tafe suna kida gangunan Fareti, a yayin da yara 'yan Makarantun Fudiyya da Islamiyyu ke taka Fareti a salo-salo.


Tutoci sun rika filfilawa sama, a yayin da matasa daga rukunin makarantun Islamiyyu suka rika saka sautin Sifiko masu amon sauti na musamman in suka rika feso baitukan yabo ga sayyida Fatima(S.A); Tituna suka rika amsawa, a yayin da 'yan gari suka rika gurguntowa gungu-gungu domin gane wa yadda Muzaharar Maulidin ke wucewa.


Iyaye Burazu ma ba a bar su a baya ba wajen taya 'yan'uwa Mata aiwatar da Muzaharar bisa jagorancin Malam Shehu Dalhatu Karkarku. Su kuwa Zana-zanan 'yan'uwa Mata(Zones) da dandalolinsu, sun fito ne a tawaga-tawaga inda kowa ya kawatar da tawagarsa da irin nasa salon fitar ta daban da inganta ta. Rukunin tawagun matasa mata kuwa, su ma sun kure tasu fitar waje fitowa zagayen, tun daga samfurin rubututtukan sunayen Sayyida Fatima(S.A) da suka rubuta a kan Banoni, Sitiku, Tutoci da Hiramai; Balam-balam sun rika yawo a sama; wadannan duk sun kayatar da zagayen.


Harisawa ko, sun raka zagayen da irin nasu Faretin na musamman, inda wasu ke saka idanu a kan abin da ke kai-komo a zagayen tare da ganin an aiwatar da shi cikin tsari da nasara.


Malama Khadija Wowo ita ce ta gabatar da jawabin rufe Muzaharar, inda a cikin jawabin nata ta ja hankalin 'yan'uwa Mata wajen riko gam-gam da dabi'un Sayyida Fatima(S.A) musamman a wajen kayutata shiga da Ibada, duba da yadda take a jinsunsu kuma suke ikirarin So, Kauna da kuma bin ta. 


Malama Wowo har wayau, ta kuma yi kira ga Burazu da su yi kokarin yin wani abu muhimmi na kyautatawa ga Matayensu a duk irin wannan lokaci na Mailidin Sayyida Zahara(S.A) ko da na yafe wani laifi ne a tsakaninsu, don nuna girmamawa da farin cikin samuwar Sayyida Fatima(S.A).


22/06/1444   15/01/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post