MU'UTAMAR KATSINA RANA TA BIYU A rana ta biyu Malama Zeenatu Ibraheem takasance mai jawabi na biyu ta gabatar da jawabi mai taken HADAFIN HARKA ISLAMIYYA


fara da cewa munsamu kanmu wata kasa da ake cewa Nigeria wanda Turawan Mulkin Mallaka suka kirkireta Malama tayi dogon bayani kan yanda Annabawa suka sha wahala tare da wasu daga cikin mabiyansu kamar yanda ya faru lokacin shehu Usman dan fodio .

  Shi shehu Usman dayazo bayayi magana bane kan mutane su karbi musulunci ba yayi kirane Akan azo a gyara dokan Allah inda shehu ya fassara kalmar La'ilaha Ilallah da cewa babu sarki sai Allah kamar yanda lokacin mulkin sarakuna shine abinda keda karfi shiyasa yayi musu magana da yaren da zasu fahimta ,kamar yanda shina sayyed ya fassarata da cewa BABU GWAMNATI SAITA ALLAH Sai hukumomi suka fahimta insa sukayi masa caa 

Malama kuma tayi bayani kan hakikanin Adalci sannan malama ta sanar damu Hakikanin kiran malam shine kafircewa tsarin kafirci da komawa tsarin Allah .

    Malaman ta tsoratar damu akan biyewa wadannan Azzaluman inda ta bayyana cewa muddin mukayi musu biyayya to za a Azabtar damu tare dasu duk da cewa sudin sunsha sharholiyarsu a duniya kai kuwa kasha wahala a duniya kuma kaje lahira ta sha Azabar Allah,idan har mutum yana da wayau to zayabi Allah inda mutum zai kasance Mai matsayi a wurin Allah idan har ka cinye dukkan jarabawoyinsa.


 Malama ta bayyana mana cewa kyawun dabi'un Sayyed da dagewa akan gaskiya sune suka sanya muka fahimci Ahlul (as)

   Sannan Malam bai boye mana komai ba cewa acikin wannan tafiya akwai bala'o'i da jarabawa idan har kana cikin wata tafiya bakaga wadannan Alamomi ba to ba Addini kakeyi ba saboda Annabawa sunshade wahala hakama manzon Allah(S) dayafi kowa daraja yasha wahalar da tafi ta kowa dan haka sadaukarwa bayin Allah itace ke tabbatar da Addini Malama tayi kira cewa yakamata mu zama masu fahimta da ganewa kafin aiaik

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post