[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Babban Bankin Najeriya wato CBN ya fitar da sanarwar fara aiwatar da musayar takardar kudi daga ranar Litinin mai zuwa, wato 23/1/23. Wannan na nufin za a tura Jami'ai zuwa lungunan kauyukan kasar nan domin a karbo tsofaffin takardun nera a bayar da sababbin kuɗin naira a hannu ba ta cikin asusun ajiyar banki ba.
CBN ta zaiyana jadawalin yadda za a gudanar da musayar; inda ta ce duk mutum daya ba za a musanya masa fiye da nera dubu goma ba (₦10,000). Idan yana da fiye da haka to za a yi amfani da katin zabe (Voter's card) ko katin dan kasa (National ID. Card) ko BVN domin a zuba masa kuɗin cikin jakar ajiya wato wallet.
Sanarwar ba ta kaiyade yawan kwanakin da za a yi ana musayar ba, sai dai ta ce mako-mako ne Jami'an za su rinka mayar da nerorin zuwa bankuna, su kuma bankuna sai su tura su zuwa CBN. Sanarwar ta jaddada cewa ba za a biya Jami'an musayar da ko kwabo ba sannan babu fifiko tsakanin kuɗin da aka bayar da wanda za a karɓa.
To idan kuwa haka ne, kenan babu wata damuwa don watan Janairu ya mutu alhali kana tare da tsaffin nerorin. Za a zo har gida a ba ka nairori.
Sai dai wani hamzari ba gudu ba, me ya sa tun yanzu masu shaguna suka fara nuna fargaban karɓar tsofaffin kuɗin ne? Me ya sa jama'a suka fara kin karɓar nerorin ne?
Wala'alla amsar wannan na tattare da rashin aminci da mutane su ke da shi dangane da lamarin ne. Mutane yau su ka sani, sanin gobe kuma sun bar wa Allah. Shi ya sa suka fara ɗaukar matakan kariya, domin an ce idan duka ya yi yawa to na kai ake karewa; iya ruwa wai an ce fidda kai! Sannan kamar mutane suna kallon bayanan CBN a matsayin tamkar mace ce mai ciki, ba a san me za ta haifa ba??
Ku a ra'ayinku, mene ne dalilin da ya sa mutane suka fara kin karɓar tsofaffin takardun kuɗi tun kafin cikar wa'adi du da cewa akwai kuma wani tsarin da aka fitar wanda zai taimaka wa mutane ta yadda ba za su yi asara ba???