Muhimmiyar Sanarwa....!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


OFISHIN JAGORA Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Tare da CIBIYAR WALLAFA Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H) 


Na sanar da dukkan al'umma cewa; wani muhimmin littafi na Tarihin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma tarihin Harkar Musulunci, wanda Sayyid Zakzaky (H) ya rubuta da kansa, (wato AUTOBIOGRAPHY) zai fito nan ba da dadewa ba.


Wannan littafi mai suna; "TARIHIN RAYUWATA, DA NA HARKAR MUSULUNCI ", shi ne irinsa na farko a tarihin Harka Islamiyyah.


Jagora (H) ne da kansu suka rubuta wannan littafi mai cike da zurfafan batutuwa daban-daban, da dimbin al'amuran da kowane dan uwa ke bukatar ya sani. Tun daga asalinsu, haihuwa da tasowarsu, karatu da fara Gwagwarmaya, da kuma marhalolin da aka rika takawa a gwagwarmaya na jarabawowi, waki'o'i, tsare-tsare a kurkuku daban-daban da fitintinu, da darussa a kan kowane gaɓan marhala. 


Littafin yana kunshe da Babi kusan 30, da Fasali 260, da Kalmomi fiye da Dubu dari biyu (200), da kuma shafuka sama da 700 cikin Juzu'i biyu.


Za a kaddamar da wannan muhimmin littafi a daidai lokacin da Jagoran Harkar Musulunci, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) zai cika shekaru 72 da haihuwa, wato a cikin watan na SHA'ABAN mai zuwa a duk fadin kasar nan.


Wannan littafi ya yaye duhu, ya samar da haske, ya fayyace hakika game da dimbin abubuwan da mafi yawan jama'a suka jahilta game da Harkar Musulunci da Jagoranta.


A cikin littafin za ka karanta dimbin abubuwan da ba ka taba sani ba game da Harkar Musulunci da rayuwar Jagora (H), duk daga Jagora da kansu.


Yana da muhimmanci sosai 'yan uwa maza da mata, kowa ya tanadi kudi don mallakar wannan littafi da babu irinsa, a daidai lokacin da za a kaddamar da shi a dukkan Da'irorin kasar nan.


Sanarwa Daga:

— Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).

Email: officeofsayyedzakzaky@gmail.com


Tare da;-


— Cibiyar Wallafa Da Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).

GSM: 080-3701-8806.


@Szakzakyoffice 

#autobiography  

11/01/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post