@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE.
- By Dr. Nazir Umar Muhammad...✍️
Matar da cikin ta baiwuce sati 8 zuwa 12 ba Sai ta fara ganin jinin kadan kadan Babu zato Babu tsammani ya za a magance wannan matsalar???
Maganin wannan matsalar ya ta'allaka kan matar da Kuma malamin lafiyar da aka samu da wannan case din.
ABUBUWAN DAYA DACE AYI MA DUK WATA MATA DATA SAMU KANTA CIKIN WANNAN YANAYIN DA KUMA ABUNDA YA DACE ITAMA TAYI DAN TAIMAKON KANTA.
- A daidai wannan lokacin likita ya dace yasan bayanan wadannan cutukan daidai lokacin da irin wannan case din yazo
- Awon malaria:- a tabbatar matar batada Malaria din
- Awon Ciki:- ayi awo nan take a tabbatar shin cikin ne, akwai shi koya zube shin Koko ma al'ada ce ba ainahin cikin bane.
- Daukan Bp:- a tabbatar da matar jinin ta Bai hau ba.
Bayan anbi wadannan matakai idan aka samu Daya daga cikin wadannan cutukan to za a Dora matsalar garesu Kai tsaye, sannan a fahimtar da Mai matsalar sauran ababen daka iya haifar da wannan matsalar kamar
Tsorata kila mace wani Abu ya Bata tsoro cikin ta zai iya zubewa.
- Accident kila mace ta samu accident
- Hard Working kila mace ta hau mashin misali anbi da ita hanyar da Babu kyau wannan zai iya Haifar da bullowar jini ga masu karamin ciki da dai sauransu.
To idan aka samu wadannan ya za a magance matsalar❓❓
Hanya ta farko da ake Dora mace akanta shine Samun wadataccen Hutu, Bai kamata wannan abun da aka gani ba yasa ayi anfani da magani a zubar da cikin Dan anga ya fara zuba yin hakan kuskure ne.
Matar da ta samu wannan da zaran abun ya faru tayi anfani da packing sannan ta samu waje ta natsu jinin zai tsaya da kansa cikin ta yaci gaba da girma.
A sani anfani da mafi yawan magunguna daidai wannan lokacin matsala ne Kuma daga karshe za a rasa cikin da fatan an karu Kuma idan akwai tambaya Ina jira.
Allah yasa mu dace.
Tags:
Cuta da Magani