[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Tare da ɗan Kogon tsira: Shehul Islami Aminu Bello
1. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabi Muhammadu SAW wai yana zage-zaage ba.
مسلم 4706
2. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai yana umurtar sashen matansa akan sashe su yi zage-zage ba.
صحيح البخاري 2581" مسلم 2442
3. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai yana fitsari a tsaye kan hanya cikin bola ba.
البخاري 224" مسلم 273
4. Ban yarda da Hadisin da ke cewa wai iyayen Manzon Allah da Baffansa wai 'yan wuta ne ba.
مسلم "203"
5. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabi Muhammadu SAW wai yana shiga gidan wata matar aure ba wai har tana yi masa kamun warkwata a kai.
البخاري (2788، 2789)، ومسلم (1912)
6. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai ya aika wasu Sahabbai sun yi wa wani mutum wai da ke zaginsa kisan gilla cikin duhun dare ba. أخرجه البخاري (3032)، ومسلم (1801
7. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW ya sa an yi wa sama da mutum ɗari uku yankan raguna ba, a Banu Ƙuraiza bayan an duba gabansu an ga gashin mararsu ya tsiro.
تخريج مشكاة المصابيح 3901 إسناده صحيح
8. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW yana zaune tare da Sahabbansa wai ya kalli wata mace da za ta wuce wai a nan take sha'awarsa ta motsa har ya tashi da sauri ya shiga gidansa ya je wa wata a cikin iyalinsa, wai kuma da ya fito ya gaya wa sahabbansa cewa kaza da kaza na aikata.
صحيح مسلم 1404
9. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW Yana zagayar matansa goma sha ɗaya cikin awa ɗaya da wanka ɗaya da rana haka da dare ya aikata haka ba.
البخاري 5215
10. Ban yarda da Hadisin da ke cewa an aiko ni domin in yanka ku ba.
صحيح الموارد : 1404
11. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai yana cewa an sanya arzikinsa karkashin inuwar mashinsa ba.
تخريج مشكلة الفقر : 24
12. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Ma'aiki SAW wai yana halartar wuraren da Shaiɗanun mutane da aljannu su ke halarta ba.
صحيح البخاري 5190
13. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW yake cewa ba: wai an sa min son mata ba.
النسائي 3939
Ibnu Hajar a Fat'hul Baariy 15/3 ya inganta shi!
14. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai ya umurci ɗaya daga cikin matansa ta shayar da wani yaro baligi nononta ba.
البخاري 4000. مسلم 1453
15. Ban yarda da Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai ya halatta jinin wata mace mai ciki da wani makaho ya yi wa kisan gilla cikin dare ba..
أبو داود 4361.
Da ire irensu duka ban yarda da su ba! In kuma yarda da su shi ne SUNNAH, to gaskiya bana yin wannan kalar Sunnar!!