Mi Nene Ma'anar January.....?




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Aliyu Samba


January shine watan farko a tsarin lissafin kwanaki da watannin Gregorian da kuma Julian wanda yake da kwanuka 31, kuma ranar farko ta watan January itace rana ta farkon kowacce shekara a lissafin gregorian. Masana na cewa watan shine watan a yafi sanyi ga wadanda ke yankunan Arewa a duniya, kuma lokacin da aka fi ɗumi a yankunan da ke kudu a duniya. A kudu, watan na zama tamkar watan July na yankin arewa a duniya. 


Kalmar January suna ne da aka samar daga sunan watan da yake zuwa daga abin bautar rumawa mai suna Janus. A addinin rumawa da tarihin asalin su, Janus shine abin bautar su da suke cewa mai tsayawa farkon al'amura, caccanzawar al'amura, lokaci, hanya, da kuma karshen al'amura. Ana sassaka gunkin sa da fuskoki guda 2 da suke nuna yana wakiltar gaba (future) da abinda ya shude (Past). [Hoton gunkin ne a kasan post] 


An hadu akan cewa sunan watan January ya samu ne daga sunan Janus Lanuarius. Wasu na kiran sa da wasu sunayen kamar Ianuspater ("Baban Janus"), Ianus Quadrifrons ("Janus mai fuska 4"), Ianus Bifrons ("Janus mai fuska biyu").


A kimiyyar Taurari kuwa ta (Astrology), January na da wata ma'anar ne daban da wannan, domin watan nana wakiltar masu dauke da taurari ne guda 2,  ana kiransu da Capricorn wanda a ilimin falaki a larabce suke cewa (Burujin Aljadyu) da kuma Aquarius da suke cewa (Burujin dullu) .


Capricorn na wakiltar mutanen da aka haifa daga 1 ga watan January zuwa 19 ga watan (Sun fara daga 21ga watan Disamba), wanda zaka same su mafi akasarin su mutane ne masu kazar kazar da kuma kokari da jajircewa, kuma da yawan su suna kaiwa ga cimma nasarori masu girma a rayuwar su. Wadanda aka haifa kuma daga 20 ga watan January zuwa 31 ga watan sune ake kira da aquarius (Kwanukan su na ƙarewa ne a 19 ga watan Fabrairu). Su aquarius mutane ne da zaka same su masu tsananin kunya da Karancin magana, suna da zuzzurfan tunani sannan suna kokari wajen adalci ga mutane ba tare da duba banbancin dake tsakanin su ba.


January yana fara wa ne da rana daya da October a mafi yawancin shekaru, tare da watan April da kuma July a shekarun da ake cewa leap year, sannan yana karewa da rana iri daya da ta karshen watan February da kuma October a mafi akasarin shekaru, da watan July a shekarar leap year. A mafi akasarin shekarun da suke kafin leap years, ko kuma leap years da suke kafin watannin shekarar da ba leap year ba,  January tana fara wa da rana irin ta farkon watan September da kuma December a shekarar dake gaba, kuma tana karewa da rana irin ta karshen watan April da December na shekarar dake gaba. Sannan tana farawa ta kuma kare da rana irin ta watan May a shekarar dake gabanin haka.


Wannan shine takaitaccen abinda zan iya wallafawa a wannan shekarar game da watan January. Allah yasa mu shiga a Sa'a ya kuma bamu albarkar dake tattare da watan. Ameen. 


©Aliyu Samba

1st January, 2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post