@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
1- M.Qariballah baya da'awa
2- M.Qaribullahi baya rubuce-rubuce
3- M.Qaribullahi baya gine-ginen makarantu da masallatai
Dukkan mai ruwa da tsaki a wannan matsalar ta Malam Abduljabar, zaka samu cewa, Aqidar da yake karewa tana da tarin makarantu da masallatai a fadin kasar nan bila adadin, amman a ɓangaren Darikar kadiriyya Basu da Komai Masallaci ko makaranta sai a iya kano ne kawai, sai kuma wadanda Malam Nasiru Kabara ya kaddamar a ɗai-ɗaikun gurare a lokacin yana raye.
Saboda haka Darikar Ƙadiriyya ta rasa gurbin Jajirtaccen shugaba akan kujerar ta mafi girma tun bayan rasuwar Malam Nasiru Kabara.
To tayaya wani Malamin zai samu wata matsala da irin wannan shugaban?
Burin su kada aji sunan Ɗarikar Ƙadiriyya a Kasar nan takowace suffa, kuma sun samu hakan daga shugabanta, To me ya rage? kawai a hade Kai dashi a karasa aikin rusa Ɗariƙar Ƙadiriyya....
Malam Abduljabar ya ɗauki turba irin ta mahaifinsa, ta hanyar ɗaga murya wajen kiran al'umma su zo zuwa ga sufanci na gaskiya, shine tsarkake janibin ma'aiki tare da kauda duk wanda zai shiga tsakanin al'umma da dabi'un Annabi tsarkaka.
Malam Abduljabar ya maida hankalinsa gun gine-ginen makarantu da masallatai da zasu fito da darajar Ɗariƙar Qadiriyya da sufanci gaɓa ɗaya, wanda da yawa matasa sun bar Ƴan damfarar malamai suna zuwa inda yake karatu, ba iya kwaryar kano ba harda kasar nan da wasu sassa na duniya baki daya.
Rubuce-rubucen sa sun karade duniya baki daya, al'umma sunga jajircewarsa ta hanyar fatattakar munafukai makiya musulunci, kuma ya samu nasarori da kyaututtukan lambar yabo a cikin gida da ma wajen kasar nan.
To Malaman da suke son ganin ƙarshen Dr.Abduljabbar sun sani wannan daukakar ba iya Malam Abduljabar bane yasameta ba har ma da Darikar kadiriyya baki ɗaya.
Saboda haka suka hada kawunansu don su kaudashi, don kauda Ɗarikar Ƙadiriyya.
Kaɗan kenan daga dalilan da yasa Malaman Maja basu da wata matsala da tsohon Shugaban Darikar kadiriyya, kuma suka hade kai dashi don kauda hasken wannan Darikar ta Kadiriyya wato Maulana Dr.Abduljabbar