MAULUDIN SAYYEEDA ZAHRA (AS): An Gabatar Da Pre-Khudba a Babban Masallacin Juma'a Na Garin Katsina.




Yau Juma'a 20 J/Thani 1444 Daidai Da 13 January,2023 Yan Uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Sun Gabatar Da Pre-Khudba a Babban Masallacin Juma'a Na Garin Katsina Domin Taya Al'ummar Musulmi Murnar Haihuwar Diyar Manzon Allah (S) Fatima Az-Zahara (AS).


Lokacin Da Yake Jawabin Sa Ga Al'ummar Musulmi Sayyeed Malam Ibrahim Mansur Bayan Kammala Sallah Juma'a Ya Bayyana Tarin Darajojin Sayyidah Zahra (AS) Da Kuma Hikimar Allah Daya Baiwa Manzon Allah (S) Sayyidah Zahra Matsayin Mace Bayan Wafatin Yan Uwanta Maza, Bayan Ya Kammala Bayani Akan Mauludin Sayyida Zahra (AS) Sayyeed Ibrahim Mansur Ya Ci Gaba Da Bayyanama Al'ummar Musulmi Da'awar Malam Zakzaky Da Kuma Manufar Kiran Da Jagora Sheikh Zakzaky (H) Yakema Wannan Al'ummar.


Bayan Ya Kammala Jawabin Sa Jama'a Sun Nuna Jin Dadin Su Akan Wannan Tunatarwa Da Kuma Bayyana Goyon Bayansu Inda Sukayita Zuwa Wajen Sayyeed Ibrahim Mansur Ana Gaisawa Cikin Farin Ciki Da Jin Dadi.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post